Alhamis 1 Oktoba 2026 - 19:31
Saƙon Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ga Taron Salla na Ƙasa karo na 33

Hauza/ Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, Ayatullah Sayyid Mujtaba Husaini Khamene’i, ya bayyana cewa sanya salla ta zama ginshiƙi kuma al’ada mai yaɗuwa a cikin al’umma, tare da ƙoƙarin kyautata yadda ake gudanar da ita, na daga cikin muhimman matakai wajen gina al’ummar Musulunci. Ya kuma jaddada cewa limaman masallatai da na sallar Juma’a ya kamata su kasance mafaka ga mutane, su saurare su, kuma su kasance masu karɓar koke-kokensu da damuwarsu.

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito daga Tehran cewa, saƙon Ayatullah Sayyid Mujtaba Husaini Khamene’i, Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, ga Taron Salla na Ƙasa karo na 33, ya kasance kamar haka:

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Ƙai

Kulawa da babban al’amari na tsayar da salla, musamman shirya taro kan salla, na daga cikin muhimman ayyukan da ya kamata a ci gaba da yi. Tun daga farkon shekarun 1990 ne aka fara wannan aiki a ƙasar, bisa ƙoƙarin Hujjatul Islam wal Muslimin Qira’ati, wanda malami ne mai ƙwazo, mai hulɗa da jama’a, malamin Alƙur’ani kuma ƙwararren mai wa’azi.

Kulawar musamman da babban Jagoran da ya gabata, wanda Allah Ya ɗaukaka matsayinsa, ya yi wa wannan al’amari, da kuma shawarwari masu muhimmanci da ya riƙa bayarwa a saƙonninsa ga tarukan salla guda 32 da suka gabata, sun ƙara nuna muhimmancin wannan hanya.

Babu shakka, yin magana ko rubutu game da salla abu ne da ya dace da koyarwar wahayi, da kalmomin Manzon Allah (SAWA) da kuma Imamai Ma’asumai (AS). Saboda haka, alkalamin mutum kamar ni bai kai matsayin yin bayani mai zurfi kan manyan ma’anoni da sirrin salla ba. Amma kasancewar muna cikin al’ummar Musulunci, da kuma irin nauyin da ke kan masu yi wa wannan al’umma hidima, musamman Jagorancin Juyin Juya Halin Musulunci, ya sa ya dace in tunatar da kaina, da al’umma da kuma jami’ai da wasu kalmomi a kan wannan batu.

Salla na daga cikin manyan ni’imomin da Allah Ya yi wa bayinsa. Ita ce ɗaya daga cikin manyan ginshiƙai da alamomin addini, kuma hanyar da kowane mutum zai iya haɗa kai da Allah kai tsaye, wanda Shi ne tushen da ba ya ƙarewa.

Salla hanya ce ta samun nasara da tsira, kuma ginshiƙi ce ta rayuwa mai kyau. Ita ce abin dogaro mai ƙarfi da ɗorewa da mutum yake amfani da shi wajen yaƙi da sha’awoyin zuciya da kuma sharrin shaidanu na duniya. Haka kuma, salla tushen ƙauna, fata, tausayi da kwanciyar hankali ce. Samun albarka da yalwar arziki daga Allah ma na daga cikin sakamakon tsayar da salla da neman gafarar Allah.

Amma salla ba aikin da ya shafi mutum shi kaɗai ba ne. Bisa koyarwar Alƙur’ani, tsayar da salla ita ce farkon alama da sakamakon shugabancin mutanen kirki. Allah Ya ce:

«اَلّذینَ اِنْ مَکَّنّاهُم فی الأرضِ اَقاموا الصَّلاة»

“Waɗanda idan muka ba su iko a cikin ƙasa, za su tsayar da salla.”

Kasancewar wannan aya ta zo kai tsaye bayan ayar da ta yi alkawarin taimakon Allah ga waɗanda suke taimakon addininsa da kuma yin jihadi a cikin Suratul Hajji, yana nuna cewa tsayar da salla, wadda take ƙarfafa ambaton Allah, bege da dogaro gare Shi, tana da muhimmiyar rawa wajen jihadi, nasara da cin galaba a fagagen gwagwarmaya, musamman irin gwagwarmayar da al’ummar Iran take fuskanta a yau.

A yau, da aka samu ƙarin damar da ƙarfin da al’ummar Iran take da shi, kowane ɗan ƙasa yana cikin waɗanda wannan umarnin Allah na tsayar da salla ya shafa:

«اَقیموا الصَّلاة»

“Ku tsayar da salla.”

Baya ga haka, duk waɗanda suke da tasiri a cikin al’umma suna da ƙarin nauyi wajen wannan al’amari. Daga cikin su akwai iyaye da iyalai, malamai da abokai, malaman jami’a da masana, fitattun mutane da mashahurai. Haka kuma dukkan cibiyoyi da hukumomin da ke da tasiri wajen gina al’adu, kamar masallatai, sallar Juma’a, makarantu, jami’o’i, cibiyoyin ilimin addini (Hauzozin ilimi), kafafen watsa labarai, masu ayyukan al’adu da zamantakewa, da kuma ƙungiyoyin jama’a, musamman waɗanda suke hulɗa da matasa da samari.

Tsayar da salla a dukkan matakai da siffofinta a cikin al’umma da ƙasar da ta ɗaga tutar Musulunci na gaskiya na Manzon Allah (SAWA), kuma ta yi alfahari da kafa tsarin mulkin Musulunci, yana daga cikin manyan al’amura.

Wannan yana da muhimmanci wajen samar da hanyar da za a bi daga matakin juyin juya halin Musulunci zuwa matakin al’ummar Musulunci. Bayan haka ne kuma za a iya kaiwa ga matakin wayewar Musulunci.

Sanya salla ta zama ginshiƙi kuma al’ada mai yaɗuwa a cikin al’umma, sannan a yi ƙoƙari gaba ɗaya wajen kyautata yadda ake gudanar da ita, su ne manyan ginshiƙai biyu na wannan yunƙuri.

Gyara da bunƙasa masallatai, da sauran matakan da za su taimaka wajen ƙara yawan sallar jam’i da ta Juma’a, tare da inganta yadda ake gudanar da su, su ne muhimman matakan da ake buƙata domin cimma wannan manufa.

A dukkan waɗannan al’amura, rawar da limaman masallatai da limaman Juma’a suke takawa tana da matuƙar muhimmanci. Ya kamata su kasance mafakar mutane, masu sauraron su, kuma masu karɓar koke-koke da damuwarsu.

Ina fatan cewa, da falalar Allah da kuma kulawa da addu’ar musamman ta shugabanmu, Imam Mahdi (Allah Ya gaggauta bayyanarsa), al’ummarmu da ƙasarmu za su samu nasara da taimakon Allah wajen tsayar da salla da kuma amfana da falaloli da albarkar da take tattare da ita.

Sayyid Mujtaba Husaini Khamene’i

9 ga Mehr, 1405 (01 ha Oktoba 2026)

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha