Kamfanin Dillancin Labaran Hauza | An halicci mutum yana da ’yancin zaɓi. Saboda haka, abubuwa daban-daban na iya sa shi ya bar bautar Allah, ya manta da ’yancinsa, kuma ya zama bawan wani. Saboda haka ne Imam Ali (A) ya ce:
««وَ لَا تَکُنْ عَبْدَ غَیْرِکَ وَ قَدْ جَعَلَکَ اللَّهُ حُرّاً.» ¹»
“Kada ka zama bawan wani, domin Allah Ya halicce ka ’yantacce.”
Ƙarin Bayani:
A kashi na biyu na wannan magana daga Nahjul-Balagha, Imam Ali (A.S) ya ce: “Allah Ya halicce ka ’yantacce.” A farkon maganar kuma ya ce: “Kada ka zama bawan wani.”
Tambaya:
Ta yaya mutumin da aka halicce shi ’yantacce zai zama bawan wani?
Wataƙila amsar tana cikin waɗannan hadisai:
««مَنْ کَرُمَتْ عَلَیْهِ نَفْسُهُ، هَانَتْ عَلَیْهِ شَهَوَاتُهُ.» ²»
“Duk wanda ya san darajar kansa, sha’awarsa ba za ta rinjaye shi ba.”
««مَنْ هَانَتْ عَلَیْهِ نَفْسُهُ فَلاَ تَأْمَنْ شَرَّهُ.» ³»
“Duk wanda bai san darajar kansa ba, kada ka aminta daga cutarsa.”
Da sauransu.
Idan muka yi tunani a kan waɗannan hadisai, za mu fahimci cewa rashin ’yanci da bautar wanin Allah suna da alaƙa da rashin mutunta kai da rashin sanin darajar kai.
Idan mutum ya san kansa kuma ya san daraja da matsayinsa na ɗan Adam, ba zai taɓa yarda da wulaƙanci ko bautar wanin Allah ba.
Iko, sha’awa, dukiya ko barazanar maƙiya ba za su iya mayar da irin wannan mutum bawa ba. Dalili kuwa shi ne, ya san cewa ainihin darajarsa tana wajen Allah. Saboda haka, ba zai yarda da wani abu da bai kai Allah da Aljanna ba.
Kamar yadda Imam Ali (A.S) ya ce:
««إِنَّهُ لَیْسَ لِأَنْفُسِکُمْ ثَمَنٌ إِلَّا الْجَنَّةَ، فَلَا تَبِیعُوهَا إِلَّا بِهَا.» ⁴»
“Ku sani, babu wani abu da ya cancanci ku sayar da kanku da shi sai Aljanna. Saboda haka, kada ku sayar da kanku da wani abu da bai kai Aljanna ba.”
Bayanan ƙasa:
1. Nahjul-Balagha, Wasiƙa ta 31.
2. Nahjul-Balagha, Hikima ta 449.
3. Tuhaful Uqul, Juzu’i na 1, shafi na 483.
4. Nahjul-Balagha, Hikima ta 456.
An shirya wannan rubutu ne a Sashen Ilimi da Al’adu na Kamfanin Dillancin Labaran Hauza.
Ra'ayinka