A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Ayatullah Sayyid Mujtaba Husaini Khamene'i, Jagoran juyin juya halin Musulunci, a cikin saƙonsa na murnar Makon Haɗin Kan Musulmi, tare da taya murnar zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah Muhammad (S.A.W.A) da Imam Ja’afar Sadik (A.S), ya bayyana cewa shirin masu mugun nufi da maƙiyan Musulunci shi ne fito da bambance-bambance fili domin raunana al’ummar Musulmi da kuma mamaye ta.
Ya kuma yi nuni da cewa yanzu an cire mayafin yaudara daga fuskar Amurka mai aikata laifuka, inda ya jaddada muhimmancin haɗin kan al’ummar Musulmi, kare juna a gaban kafirci, da kuma ƙara haɗin gwiwa a fannoni daban-daban na rayuwa ta zahiri da ta ruhaniya.
Ya kuma jaddada wa sarakuna da shugabannin ƙasashen Musulmi cewa: “Shugabannin masu aikata laifuka na Amurka da tsarin sahyoniya na ƙarya, maƙiyan rantsuwa ne na haɗin kan Musulmi da dukkan al’ummar Musulmi, ciki har da al’ummomin Yammacin Asiya da Arewacin Afirka. Don haka, ku gane ainihin maƙiyinku kuma ku tunkari shirinsa.”
Haka kuma, ya yi nuni da yadda darussan haɗin kan Musulunci suka samu karɓuwa yadda ya kamata a ƙasar Iran, inda ya sake ba wa daukacin al’ummar Iran shawarar cewa kada su taɓa barin wani sabani ya bayyana a tsakaninsu.
Ga cikakken saƙon Jagoran juyin juya halin Musulunci:
Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin ƙai.
“Muhammadu Manzon Allah ne, kuma waɗanda suke tare da shi masu tsanani ne a kan kafirai, masu jin ƙai ne a tsakaninsu.”
Ina taya al’ummar ƙasar Iran mai daraja da kuma babbar al’ummar Musulunci murnar ranakun haihuwar fitila mafi girma, mafificin halittu, fitila mai haskakawa, zaɓaɓɓen Allah, birnin ilimi, Rahamar talikai, Manzon Allah mai daraja, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da Alayensa, da kuma ɗansa tsarkakke kuma mai kyawawan halaye, hujjar Allah cikakkiya, Imam Ja’afar Sadik, tsira da amincin Allah su tabbata gare shi.
Tun daga lokacin da hasken kasancewar Manzon Allah na ƙarshe ya fito a Makka mai daraja, hangen nesa na samun farin cikin ɗan Adam, wanda ya dogara da cikar bauta da biyayya ga Allah Maɗaukaki, ya ƙara haskakawa. Ruhohin Annabawa, mala’ikun Allah da tsarkaka suka cika da farin ciki, yayin da shaidanun mutane da aljanu suka ciji yatsunsu saboda fushi, nadama da baƙin ciki.
Domin mafi girman halittar Allah a cikin dukkan duniyoyin halitta marasa iyaka yana zuwa duniya, kuma nan ba da daɗewa ba, da tufafin Annabci da kasancewarsa Annabi na ƙarshe, tare da riƙe da Alƙur’ani Mai girma da kuma aikin shiryar da ɗan Adam ta kowane fanni, zai fara tsara tafiyar babban ayarin bil’adama zuwa ga bautar Allah da kuma samun kamala zuwa gare Shi.
Rayuwar wannan Manzo da Wasiyyansa Ma’asumai gaba ɗaya darasi ne na shiriya da bauta; darasi ne na sani da ƙauna; darasi ne na akida da jihadi; darasi ne na rayuwa da kyawawan ɗabi’u na mutum da na al’umma; darasi ne na amana da gaskiya; darasi ne na ɗaukaka da mutunci; darasi ne na ilimi da aiki; darasi ne na rahama da tsauri; darasi ne na adalci da daidaito; kuma darasi ne na haɗin kai da ‘yan’uwantaka.
Duk yadda aka ƙara koyon waɗannan darussa da aiki da su, hakan zai ƙara sauƙaƙa wa ‘ya’yan Adam kai wa kololuwar farin ciki da arziki.
Mun yi imani cewa tsarkakakkiyar ruhin Manzon Rahama, da kuma tsarkakan ruhohin Wasiyyansa da hujjojin Allah masu tsarki, tsira da amincin Allah su tabbata gare shi da su baki ɗaya, koyaushe suna lura da al’amuran Musulmi da al’ummar Musulmi, suna shiryar da su kuma suna tausaya musu.
Idan wani kuskure ya faru daga ‘ya’yan wannan uba mai girma da tausayi, hakan yana ɓata musu rai; kuma duk lokacin da Musulmi suka aiwatar da darussansu da umarninsu, zukatansu masu albarka suna farin ciki.
Yanzu Musulunci da mabiyansa, bayan sun tsallake lokuta masu tsanani da cike da rikice-rikice, kuma bayan sun bi matakai daban-daban na sauƙi da wahala tun daga farkon Musulunci har zuwa yau, sun kai wani matsayi mai muhimmanci da zai ƙayyade makomarsu.
A yau Musulmi na iya taka muhimmiyar rawa wajen tsara tarihi. A yau rana ce da hangen nesa na nasarar ƙarshe ta gaskiya a kan ƙarya, da Musulunci a kan kafirci, ya fi kowane lokaci a baya kusantar zama abin da za a gani a zahiri.
Sharadin farko shi ne haɗin kan Musulmi
Sharadin farko na wannan babban al’amari shi ne haɗin kan Musulmi. Haɗin kan Musulmi a gaban kafircin duniya, wata dabara ce ta Alƙur’ani kuma koyarwa ce ta asali daga Musulunci na gaskiya na Annabi Muhammad, tsira da amincin Allah su tabbata gare shi da Alayensa, ba wani abu ba ne na sama-sama ko na wucin gadi.
Ma’anar haɗin kai ita ce a matakin al’umma gaba ɗaya, abubuwan da Musulmi suke daidaitawa a kansu su zama ginshiƙi da tushe.
Tabbas, ana ƙoƙarin, ta hanyar hujja da kuma tare da kiyaye dukkan abubuwan da suka shafi ‘yan’uwantaka da haɗin kai, kamar yadda koyarwar Alƙur’ani take nunawa, a cikin cikakkien zaman lafiya da fahimtar juna, a mayar da wuraren da ake saɓani a kansu zuwa wuraren haɗin kai.
Abin da yake tabbatacce shi ne cewa dukkan Musulmi a cikin al’ummomin Musulmi, yayin fuskantar kafircin duniya, dole ne su sanya wannan ƙa’idar Alƙur’ani ta “masu tsanani a kan kafirai, masu jin ƙai a tsakaninsu” a matsayin tushen tunani, magana da aiki. Ta haka ne za a samu haɗin kai da haɗin kan Musulunci.
A duk lokacin da ɗaya daga cikin waɗannan ɓangarorin saƙon sama ya yi nisa da aikace-aikacen Musulmi, za su nisanta daga wannan matsayi na ɗaukaka da suka cancanta a cikin duniyar Musulunci. Wannan ƙa’ida ce da ba ta taɓa canzawa ba.
Wannan ƙa’ida na daga cikin muhimman ginshiƙai da saƙonnin juyin juya halin Musulunci. Tarihin gudanar da Makon Haɗin Kai na farko ya koma zuwa watan Esfand na shekarar 1356 ta kalandar hijira ta Shamsiyya (Fabrairu, 1978), a lokacin gwagwarmaya da gwamnatin zaluncin Shah Pahlavi. A lokacin ne babban Jagora shahidi, Allah Ya ɗaukaka matsayinsa, yayin da yake zaman gudun hijira a Iranşahr, ya gabatar da wannan tunani, kuma Shi’a da Sunna suka karɓe shi.
Ba da daɗewa ba bayan nasarar juyin juya halin Musulunci, bisa hikimar wanda ya kafa Jamhuriyar Musulunci, Imam Khumaini, Allah Ya tsarkake sirrinsa, aka sanya “Makon Haɗin Kai” a matsayin biki a hukumance.
Da falalar Allah Maɗaukaki, batun haɗin kai tsakanin dukkan ‘yan al’ummar Iran Musulmi ya zama misali mai nasara a tsakanin al’ummar Iran, kuma makircin maƙiya bai yi tasiri sosai wajen lalata wannan haɗin kai ba.
Amma babu shakka masu mugun nufi koyaushe suna sa ido kan wannan babbar ni’ima. Abin da ke ba su fata shi ne fito da bambance-bambance fili.
Bambance-bambancen akida da mazhaba, duk da cewa suna daga cikin muhimman abubuwan da maƙiyan Musulunci ke nufi kuma ke matuƙar dogaro da su, ba zai tsaya a kansu kawai ba.
Suna ƙoƙarin mayar da kowane irin bambanci na ƙabila, al’ada, zamantakewa, tattalin arziki, siyasa da ƙasa zuwa uzurin haifar da sabani tsakanin al’ummar Musulmi a Iran da kuma kowace ƙasar Musulmi, domin daga wannan ɓangaren su kalli yadda al’ummar Musulmi ke wargajewa kuma ƙarfinsu ke raguwa, sannan a lokacin da ya samu dama ya yi musu mulkin mallaka.
Umarnin Alƙur’ani Mai girma a irin waɗannan lamura shi ne: “Kada ku yi jayayya, har ku raunana, ƙarfin ku ya tafi.”
Saboda haka, duk mutumin da yake a kowane matsayi, idan ya aikata wani abu da zai haifar da rarrabuwar kai tsakanin Musulmi kuma ya jefa sabani a cikin al’ummar Musulmi, ko ya sani ko bai sani ba, ko da gangan ko ba da gangan ba, to ya taimaka wajen cika manufar maƙiyan Musulunci.
Ta yaya mutum zai iya danganta irin wannan aiki ga jahilci da rashin sani a wannan zamani, alhali kuwa azzaluman duniya, a kan gaba daga cikinsu akwai Amurka mai aikata laifuka, sun cire dukkan mayafin yaudara da na bogi daga munanan fuskokin manufofinsu na mulkin mallaka da shirye-shiryensu na danniya da neman mamaye duniya, kuma sun cire safar hannu mai laushi ta yaudara, suka nuna wa duniya baki ɗaya faratan hannunsu masu jini?
Yanzu lokaci ne da Musulmi za su yi tunani
Yanzu lokaci ya yi da Musulmi za su yi tunani sosai kuma su kalli abubuwan da suke faruwa da ƙarin zurfi.
Idan Musulmi za su kasance hannu ɗaya, suna matse dunƙulen hannunsu da ƙarfi, shin da al’ummar Falasɗinu za ta kasance cikin rashin kariya, tana fuskantar zalunci da laifukan mamaya?
Kuma da a ce al’ummomi da gwamnatocin da suke zaune a gabar Tekun Fasha sun haɗa kansu a ƙarƙashin tutar Musulunci, shin wasu ‘yan iska marasa asali kuma lalatattu da suka zo daga dubban kilomita za su sami ƙarfin yin kwadayin ƙasashensu da dukiyoyinsu?
Shawarata mai ƙarfi kuma mai maimaituwa ga shugabannin ƙasashen Musulmi, musamman ƙasashen yankin Yammacin Asiya da ƙasashen da ke gabar Tekun Fasha, ita ce: Ku gane ainihin maƙiyinku, ku fahimci shirinsa, sannan ku tunkare shi.
Maganin matsalolin al’ummar Musulmi shi ne haɗin kai, abota da taimakon juna wajen ayyukan alheri.
Shugabannin masu aikata laifuka na Amurka da tsarin sahyoniya na ƙarya, maƙiyan rantsuwa ne na wannan haɗin kai da abota.
Ba wai maƙiyan Jamhuriyar Musulunci da al’ummar Iran da babbar ƙungiyar gwagwarmayar Musulunci kaɗai ba ne; a’a, suna gaba da dukkan al’ummar Musulmi, ciki har da al’ummomin Yammacin Asiya da Arewacin Afirka.
Har ma shugabannin waɗannan ƙasashe, waɗanda da yawa daga cikinsu ana ɗaukar su a matsayin abokan aikinsu, ba a ware su daga wannan ƙiyayya ba.
Kamar yadda raini a fili da amfani da kalamai marasa kyau ga wasu daga cikin shugabannin ƙasashen Musulmi da shugabannin masu girman kai suka yi, yana nan a cikin tunanin ku da namu na baya-bayan nan.
Darussa uku na haɗin kai
Darasi mai muhimmanci na haɗin kai da kauce wa sabani shi ne darasi na farko na koyarwar Musulunci game da yadda za a mu’amalanci maƙiyi da aboki.
Amma darasi na biyu shi ne kare juna a gaban kafirci, yayin da darasi na uku shi ne nau’o’in haɗin gwiwa da ƙara ƙarfin juna a fannoni daban-daban na rayuwar zahiri da ta ruhaniya ta Musulmi, ta fuskar dukiya, tsaro, ilimi da ci gaba.
Ƙarshen wannan tafiya shi ne kai wa ga sabuwar wayewar Musulunci.
Saboda haka, haɗin kan Musulmi shi ne ginshiƙin farko na samun wannan wayewar Musulunci mai daraja da rinjaye.
Wannan tsarin tunani da fahimta, wanda burinmu ga duniyar Musulunci yake ƙunshe a cikinsa, ya samu aiwatuwa zuwa wani mataki mai karɓuwa a ƙasar Iran mai daraja.
Saboda haka, ina sake ba wa dukkan al’ummar Iran shawara cewa kada su taɓa barin wani sabani ya bayyana a tsakaninsu.
A ƙarshe, ina fatan ta hanyar ceton Manzon Allah mai daraja da zuriyarsa tsarkaka, tsira da amincin Allah su tabbata gare shi da su, inuwar rahama da albarkar falalar Allah za ta mamaye al’ummomin Musulmi, kuma su ci gaba da hawa matakan ci gaba da ɗaukaka, mataki bayan mataki, fiye da yadda suke a baya, a ƙarƙashin aiwatar da umarnin Allah Maɗaukaki.
Wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Sayyid Mujtaba Husaini Khamene'i
8 ga Shahriwar 1405
17 ga Rabi’ul Awwal 1448
Ra'ayinka