Kamfanin Dillancin Labaran Hauza | Wane irin sauye-sauye da ƙalubale ne suka kasance cikin rayuwar Imam Hasan Askari (A.S)?
Amsa a taƙaice:
Imam Hasan Askari (A.S), Imami na goma sha ɗaya daga cikin jagororin Shi’a, an haife shi a shekara ta 232 bayan Hijira. Mahaifinsa shi ne Imam Hadi (A.S), yayin da mahaifiyarsa take wata baiwar Allah mai tsoron Allah da nagarta mai suna “Hadisa”, wadda wasu suka kira ta da “Sausan”.
Bisa umarnin halifan Abbasawa, Imam Hasan Askari (A.S) ya zauna a birnin Samarra, musamman a unguwar “Askar”, cikin tilasci. Saboda haka aka danganta masa sunan “Askari”.
Yana da shekaru 22 lokacin da mahaifinsa ya yi shahada. Tsawon lokacin imamancinsa ya kasance shekaru shida, kuma ya rasu yana da shekaru 28 a shekara ta 260 bayan Hijira. An binne shi a gidansa da ke Samarra, kusa da kabarin mahaifinsa.
A cikin gajeren lokacin imamancinsa, Imam Hasan Askari (A.S) ya yi zamani da halifofin Abbasawa guda uku, waɗanda su ne:
1. Al-Mu’tazz Billah (252–255 H)
2. Al-Muhtadi Billah (255–256 H)
3. Al-Mu’tamid Billah (256–279 H)
Rayuwar mahaifiyar Imam Hassan Askari (A.S)
Mahaifiyar Imam Hassan Askari (A.S), wato Hadisa, ta kasance mace mai ibada, ilimi da fahimtar addinin Musulunci. Bayan shahadar Imam Hasan Askari (A.S), ta kasance mafaka kuma abin dogaro ga Shi’a a wani lokaci mai cike da rikici, tsoro da tashin hankali.
Dalilin da ya sa aka kira shi “Askari”
Saboda halifan Abbasawa ya tilasta wa Imam Hassan Askari (A.S) zama a Samarra, a wani yanki da ake kira Askar, yasa aka fi saninsa da sunan “Askari”. Daga cikin shahararrun laƙabansa akwai “Naƙi” da “Zaki”, yayin da alkunyarsa take “Abu Muhammad”.
Halifofin Abbasawa da zaluncinsu
A lokacin imamancin Imam Hassan Askari (A.S), halifofin Abbasawa uku sun kasance masu mulki. Waɗannan halifofi sun kasance masu tsanani wajen danniya da zalunci.
A farkon kafuwar daular Abbasawa, sun yi iƙirarin cewa suna goyon bayan zuriyar Ali (A.S), kuma sun ce sun tashi ne domin ɗaukar fansa kan zaluncin da aka yi wa Alawiyyawa a hannun Banu Umayya. Sai dai bayan sun samu iko, suka yi watsi da alkawuran da suka yi wa mutane, suka fara zalunci da mulkin danniya kamar halifofin Banu Umayya, ko ma fiye da su.
Matsayin Imam Hassan Askari (A.S)
Saboda haka, Imam Hassan Askari (A.S) ya karɓi nauyin jagorancin Shi’a a wani lokaci mai matuƙar wahala, inda halifofin Abbasawa suka tsananta sa ido da matsin lamba ga Imaman Ahlul-Baiti (A.S) da mabiyansu. Duk da gajeren lokacin imamancinsa, ya taka muhimmiyar rawa wajen kare akida da jagorantar al’ummar Shi’a har zuwa shahadarsa a shekara ta 260 bayan Hijira.
Ra'ayinka