Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito cewa Hujjatul Islam wal Muslimin Ridha Yusufzade, mai ba da shawara kan harkokin iyali, yayin da yake amsa tambaya game da rashin mutunta juna tsakanin ma’aurata a cikin gida da kuma a bainar jama'a, ya jaddada muhimmancin girmamawa a matsayin mafi girman buƙatar ɗan Adam, sannan ya gabatar da hanyoyi huɗu na aiki domin gyara dangantakar aure.
Tambaya: Idan mutum ya girmama abokin zamansa amma shi kuma bai rama wannan girmamawar ba, me ya kamata ya yi? Mijina ko matata ba ya girmama ni ko a gida ko a bainar jama'a. Yana mu'amala da ni kamar baiwa ko kuyanga. Me ya kamata in yi?
Amsar Hujjatul Islam wal Muslimin Ridha Yusufzade
Yaya ya kamata a yi mu'amala da rashin girmamawa?
Mun faɗa cewa daraja da girmamawa su ne mafi muhimmancin buƙatun ɗan Adam. Kuma idan akwai wata alaƙa da muke son a girmama mu a cikinta, to iyali ne ya fi dacewa da hakan.
Nazarin Matsalar
Yana da matuƙar muhimmanci dukkan 'yan uwa su riƙa nunawa juna wannan darajtawa da girmamawa.
Tambayar nan ta fito ne daga bakin mutumin da yake fuskantar raini da rashin darajtawa, har yake cewa: "Kamar ni baiwarsa ko kuyangarsa ce."
Zamanin bautar bayi da kuyangi ya shuɗe tun ƙarni da dama da suka gabata, kuma irin wannan yanayi yana cutar da kowa.
Lokacin da ba na girmama abokin zamana, shi ma yanayinsa yana lalacewa, kuma dangantakar aure tana lalacewa. Idan dangantaka ta lalace, wa zai amfana? Wa yake son rayuwa cikin mummunar alaƙa?
Wannan wani zagaye ne na aiki da martani. Idan na ɓata wa abokin zamana rai, wannan ɓarnar za ta dawo gare ni ta hanyar yadda muke mu'amala da juna. Don haka mutumin da yake wulaƙanta abokin zamansa shi ma yana cutar da kansa, domin dangantakar auren ta lalace.
To, me ya kamata a yi?
Hanya ta Farko: Ka Ci Gaba da Yin Abin da Ya Dace
Kuskuren wani ba ya halatta mu yi kuskure. Ana cewa: "Abin da ke cikin tulu shi ne yake zubowa."
Ni abin da nake son mutane su gani daga gare ni shi ne girmamawa. Ko da wasu ba sa girmama ni, hakan ba hujja ba ce da zan aikata abin da bai dace ba. Zan ci gaba da aikata abin da ya dace. Kuma ya kamata mu sani cewa kyakkyawan hali ma yana haifar da kyakkyawan sakamako, yana shiga cikin tsarin dangantaka kuma yana taimakawa wajen gyara ta.
Hanya ta Biyu: Bayyana Ji da Mayar da Martani Ba Tare da Zargi Ba
A lokacin da dangantakarku take cikin yanayi mai kyau, ka bayyana wa abokin aurenka yadda kake ji. Misali ka ce: "Wani lokaci ina jin kamar ana mu'amala da ni kamar baiwa." Mayar da irin wannan martani yana da amfani sosai, amma da sharadin kada ya kasance na zargi.
Idan ka fara magana da kalmar "Kai..." ko "Ke...", kamar: "Kai kullum kana wulaƙanta ni," "Kana kallona kamar baiwarka," "Kana yi min haka a gaban mutane," to ɗayan zai shiga yanayin kare kansa, kuma ba zai saurari maganarka ba.
Amma idan ka ce: "Ni ina jin haka..." za ka motsa jin tausayinsa da tausayi a zuciyarsa.
Lura:
Kada ka yi tsammanin cewa da zarar ka bayyana yadda kake ji sau ɗaya, halinsa zai canza nan take. Wannan yana buƙatar haƙuri.
Hanya ta Uku: Ka Faɗi Abin da Kake So a Yi, Ba Abin da Ba Ka So ba
Bayan ka yi amfani da salon "Ni ina jin...", kada ka ce wa abokin aurenka abin da kada ya yi, sai dai ka faɗa masa abin da kake so ya yi.
Ka bayyana buƙata a sarari. Misali: Ina so idan muna gaban mutane ka kira ni da "Hajiya wance" ko "Uwargida wance." Idan kana son wani abu daga gare ni a gaban mutane, ka fara da cewa "Don Allah." Idan kana magana da ni a cikin jama'a, ka ce: "Hajiya wance, don Allah ki yi wannan."
Ka fara da abin da kake son a yi (yi wannan), ba da abin da ba ka son a yi (kada ka yi wannan) ba. Ku ci gaba a hankali, mataki-mataki, tare da haɗin kai.
Hanya ta Huɗu: Ka Fahimci Buƙatun da Ba a Biya wa Abokin Aurenka
Shin akwai wata buƙata da abokin zamanka yake da ita amma ba a biya masa ba?
Sau da yawa ana iya gane buƙatun mutane ta hanyar yawan gunaguni da korafe-korafensu. Lokacin da mutum yake yawan gunaguni, a zahiri yana bayyana wata buƙata ce da yake da ita, amma cikin salon yara — kamar ƙaramin yaro mai yunwa wanda yake kuka. Wannan hali na yara yana ci gaba da kasancewa a cikin mutum har bayan ya girma.
Saboda haka, ka yi ƙoƙarin gano: Mene ne yake damunsa? Wace buƙata ce ba a biya masa ba? Wane gibi ne yake cikin rayuwarsa?
Ka taimaka wajen cike wannan gibi, zai samu natsuwa.
Mutane idan ba a biya musu wasu muhimman buƙatunsu ba, sukan zama marasa haƙuri, kasancewa cikin fushi, kuma wani lokacin sukan yi mu'amala da wasu ta hanyar da ba ta dace ba.
Saboda haka ka yi ƙoƙarin gano "ina ne yake jin ciwo?" wanda yake sa ya riƙa nuna irin wannan hali.
Ra'ayinka