A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, ana gabatar muku da jerin bahasosin Mahdawiyya mai taken "Zuwa Ga Al'umma Mai Manufa", da nufin yaɗa koyarwa da ma'arifofi masu alaƙa da Imam Mahadi (A.F.), ga ku masu ilimi da daraja.
Daya daga cikin batutuwan da aka dade ana tattaunawa a cikinsu a bahasin Mahdawiyya shi ne hukuncin mubarizozi da gwamnatocin zamanin gaiba kafin juyin juya halin duniya na Imam Mahdi (A.F.). Wasu, suna jingina da wasu ruwayoyi, sun yi zato cewa duk wani yunkuri na yaƙi da shugabanni azzalumai kafin bayyanar Imam Mahdi (A.S.) haramun ne. Saboda haka suke adawa da duk wani kira na neman adalci, suna kuma kiran ta da dagutu.
A nan za mu yi taƙaitaccen nazari kan ruwayoyin da suka shafi yunkurin kafin bayyanar Imam Mahdi (A.S.).
– Kiran Masu Tutar Gwagwarmaya Kafin Bayyanar Imam da Dagutu
Wasu daga cikin waɗannan ruwayoyi sun yi hukunci bai-ɗaya kan duk wani tawaye ko ɗaga kowace tuta kafin tashin Imam Mahdi (A.F.), suna bayyana mai ɗaga tutar a matsayin dagutu ko mushriki. Ga ruwayoyi biyu:
Imam Ja'afarus Sadiƙ (A.S.) ya ce:
«کُلُّ رایَةٍ تُرْفَعُ قَبْلَ قِیامِ القائِمِ فَصاحِبُها طاغُوتٌ یُعْبَدُ مِنْ دُونِ اللّهِ عَزَّوَجَلَّ.»
"Duk wata tuta da aka ɗaga kafin tashin Al-Qa'im, mai tutar dagutu ne da ake bauta masa ba Allah Maɗaukaki ba." (Al-Kafi, juzu'i na 8, shafi na 295).
Haka kuma Imam Muhammad Baƙir (A.S.) ya ce:
«کُلُّ رایَةٍ تُرْفَعُ قَبْلَ رایة القائِمِ صاحِبُها طاغُوتٌ.»
"Kowace tuta da aka ɗaga kafin tutar Al-Qa'im, mai ita Dagutu ne." (Al-Ghaiba na Nu'umani, shafi na 114).
Baya ga matsalolin isnadi da ke cikin waɗannan ruwayoyi, ɗaya daga cikin masu bincike ya rubuta cewa kira iri biyu ne:
1. Kiran gaskiya: Wato kira zuwa ga tsayar da gaskiya da mayar da jagorancin al'umma ga Ahlul Baiti (A.S.), kuma wannan kira Imamai Ma'asumai sun amince da shi.
2. Kiran ƙarya: Wato kira domin ɗaukaka kai. Abin da ake nufi da "kowace tuta" a ruwayar shi ne irin wannan kira na biyu, wato kira da yake a gaban ko sabanin kiran Ahlul Baiti (A.S.), ba wanda yake cikin tafarkinsu ba. Saboda haka duk wata gwagwarmaya da aka yi domin kare hurumin Ahlul Baiti (A.S.) da kuma kiran mutane zuwa gare su, ba ta shiga cikin abin da wannan ruwaya ta haramta.
Sai dai ana iya cewa wannan hadisi yana nuna cewa duk wata gwagwarmaya kafin tashin Imam Mahadi (A.F.) ba ta halatta ba, ko da kuwa kira ne na gaskiya.
Na farko: Ana ganin waɗannan ruwayoyi suna magana ne kan wasu mubarazozi na wani lokaci na musamman, ba wai suna magana ne kan dukkan gwagwarmaya ba. Saboda haka ma'aunin gaskiya da ƙarya shi ne kira zuwa tafarkin gaskiya.
Na biyu: Ruwayoyi da dama daga Imamai (A.S.) sun tabbatar da wasu gwagwarmaya da za su faru kafin bayyanar Imam Mahdi (A.F.), har ma sun ƙarfafa mutane su bi su, kamar tutar Yamani. (Najmuddin Tabasi, Ta Zuhur, juzu'i na 1, shafi na 78).
Imam Khumaini (Q.S) ya mayar da martani ga masu amfani da waɗannan ruwayoyi wajen ƙin kafa gwamnatin Musulunci, yana cewa: "Waɗannan hadisai ba su da alaƙa da kafa gwamnatin adalci ta Allah wadda kowane mai hankali ya san wajibcinta. A cikin ruwayar farko akwai yiwuwar tana magana ne kan alamomin bayyanar Imam Mahdi (A.F.), tana nufin tutocin da ake ɗagawa da sunan Imamanci kafin tashinsa ba su da inganci. Ko kuma tana yin hasashen gwamnatocin da za su kasance kafin bayyanarsa, waɗanda ba za su cika aikinsu yadda ya kamata ba." (Kashful Asrar, shafi na 225).
A wani wuri kuma ya ce: "Waɗannan ruwayoyi suna magana ne kan duk wanda ya ɗaga tuta da sunan Mahdiyanci kafin Imam Mahadi."(Sahifatul Imam, juzu'i na 21, shafi na 14).
– Rashin Nasarar Gwagwarmaya Kafin Bayyanar Imam
Wasu ruwayoyi suna bayyana cewa gwagwarmaya kafin tashin Imam Mahdi (A.F.) ba za su yi nasara ba. Wasu sun fahimci hakan da cewa kafa gwamnatin Musulunci kafin bayyanarsa ba ta halatta ba, domin gwagwarmayar da ba ta da amfani abin ƙi ne a mahangar hankali.
Daga cikin ruwayoyin akwai maganar Imam Sajjad (A.S.):
«وَاللَّهِ لایَخْرُجُ واحِدٌ مِنَّا قَبْلَ خُرُوجِ القائِمِ علیهالسلام اِلاّ کانَ مَثَلُهُ مَثَلَ فَرْخٍ طارَ مِنْ وَکْرِهِ قَبْلَ اَنْ یَسْتَوِی جَناحاهُ فَاَخَذَهُ الصِّبْیانُ فَعَبَثُوا بِهِ.»
"Na rantse da Allah! Babu wani daga cikinmu da zai yi tawaye kafin tashin Al-Qa'im face misalinsa kamar ɗan tsuntsu ne da ya tashi daga gidansa kafin fikafikansa su ƙarfafa, sai yara su kama shi suna wasa da shi." (Al-Kafi, juzu'i na 8, shafi na 264).
Wasu sun fitar da hukunci cewa kafa gwamnatin Musulunci ba kawai ba ta da amfani ba ce, har ma tana jawo wahala ga Ahlul Baiti (A.S.), don haka ya kamata a daina ƙoƙarin kafa gwamnati kafin bayyanar Imam Mahdi (A.F.).
Sai dai, baya ga matsalolin isnadi, jingina da wannan ruwaya ba daidai ba ne saboda dalilai masu zuwa:
Dalili na farko: Ruwayar ba ta zo ne domin ta hana asalin yin gwagwarmaya ba, sai dai tana magana ne kan rashin samun nasara. Idan za a ce tana hana gwagwarmaya gaba ɗaya, to hakan zai haɗa da gwagwarmayar Imam Husaini (A.S.) a kan Yazid, da ta Zaidu bn Ali da Husain bn Ali (Shahid Fakh) da sauransu, alhali babu shakka Imamai sun tabbatar da waɗannan gwagwarmaya.
Imam Ja'afarus Sadiƙ (A.S.) ya ce game da Zaidu Shahidi:
«وَ لَا تَقُولُوا خَرَجَ زَیْدٌ فَإِنَّ زَیْداً کَانَ عَالِماً وَ کَانَ صَدُوقاً وَ لَمْ یَدْعُکُمْ إِلَی نَفْسِهِ إِنَّمَا دَعَاکُمْ إِلَی الرِّضَا مِنْ آلِ مُحَمَّدٍ علیهم السلام وَ لَوْ ظَهَرَ لَوَفَی بِمَا دَعَاکُمْ إِلَیْهِ إِنَّمَا خَرَجَ إِلَی سُلْطَانٍ مُجْتَمِعٍ لِیَنْقُضَه.»
"Kada ku ce Zaidu ya fita (ya yi tawaye), domin Zaidu malami ne kuma mai gaskiya. Bai kira ku zuwa ga kansa ba, ya kira ku ne zuwa ga yardar Alu Muhammad (A.S.). Da ace ya yi nasara, da ya cika alkawarin da ya yi muku. Ya tashi ne domin ya rusa wata gwamnati mai ƙarfi." (Al-Kafi, juzu'i na 8, shafi na 264).
Dalili na biyu: Rashin samun nasara ba hujja ba ce ta cewa ba wajibi ba ne mutum ya yi abin da ya hau kansa. Misali, a Yaƙin Siffin an yaɗa cewa Mu'awiya ya mutu. Mutane suka yi farin ciki. Sai Imam Ali (A.S.) ya ce: "Na rantse da Allah wanda raina yake hannunsa, Mu'awiya ba zai mutu ba har sai mutane sun amince da shi." Sai aka tambaye shi: "To idan haka ne, me ya sa kuke yaƙarsa?"
Sai ya amsa:
«اَلْتَمِسُ العُذْرَ بَینی وَ بَیْنَ اللَّهِ.»
"Ina neman uzuri ne tsakanina da Allah." (Ibn Shahr Ashub, Al-Manaqib, juzu'i na 2, shafi na 259). (1)
Wannan ruwaya da makamantanta suna nuna cewa wajibi ne Musulmi ya aikata abin da Allah ya ɗora masa, ba tare da jiran tabbacin samun sakamakon da yake so ba.
Dalili na uku: A wasu ruwayoyi an yi bushara da wasu gwagwarmaya kafin tashin Al-Qa'im waɗanda za su zama share fage ga gwamnatin Imam Mahadi (A.F.). Babu shakka wannan yana nuna cewa sun yi nasara ta wata fuska. Mafi shahara daga cikinsu shi ne fitowar Yamani, wanda ruwayoyi da dama suka bayyana tutarsa a matsayin mai shiriya.
Dalili na huɗu: Idan waɗannan ruwayoyi suna hana yaƙi da zalunci da fasadi gaba ɗaya, hakan zai saɓa wa ayoyin Alkur'ani game da jihadi, umurni da kyakkyawa da hani daga mummuna, da kuma tarihin rayuwar Imamai Ma'asumai (A.S.).
– Yin Shiru da Zama a Gida
Wasu ruwayoyi suna umurtar mutane da yin shiru da zama lafiya, tare da hana shiga kowace gwagwarmaya kafin alamomin bayyanar Imam su tabbata.
Misali, Imam Ja'afarus Sadiƙ (A.S.) ya ce wa Sadair:
«یا سَدیرُ اِلْزَمْ بَیْتَکَ وکُنْ حِلْساً مِن اَحْلاسِهِ وَاسْکُنْ ما سَکَنَ اللَّیْلُ وَالنَّهارُ فَاِذا بَلَغَکَ اَنَّ السُّفْیانِیَّ قَدْ خَرَجَ فَارْحَلْ اِلَیْنا وَلَوْ عَلی رِجْلِکَ.»
"Ya Sadair! Ka zauna a gidanka, ka manne da gidanka, ka yi shiru muddin dare da rana suna cikin natsuwa. Amma idan ka ji cewa Sufyani ya fito, to ka zo gare mu ko da a kan ƙafafunka ne." (Al-Kafi, juzu'i na 8, shafi na 264).
Wasu suna ganin wannan hukunci ya shafi kowa har sai Sufyani ya fito.
Amsa ita ce: Faɗaɗa wannan hukunci zuwa ga kowa a kowane zamani yana buƙatar tabbacin cewa Imam bai yi magana ne ga Sadair saboda wani yanayi na musamman ba.
Saboda haka, ko da an ɗauka cewa wasu daga cikin waɗannan ruwayoyi ingantattu ne, babu ɗaya daga cikinsu da zai iya rusa halaccin kafa gwamnati ko yin gwagwarmaya a zamanin gaiba. Abin da suke yi shi ne yin Allah wadai da gwagwarmayar da ba ta cika sharuɗɗan shari'a ba ko kuma wadda aka yi saboda son rai da manufofi marasa kyau.
Saboda haka, idan wata gwagwarmaya ta kasance bisa sharuɗɗan shari'a, ƙarƙashin jagorancin shugaba adali (Faƙihi), kuma manufarta ta ginu ne bisa koyarwar Musulunci, to za ta zama share fage ga tashin Imam Mahadi (A.F.). Ba wai kawai ba za a hana ta ba, a wasu lokuta ma yin ƙoƙarin kafa irin wannan gwamnati zai zama wajibi.
Wannan tattaunawa za ta ci gaba...
An ciro daga littafin "Darsnameh Mahdaviyyat" na Khudamurad Salimiyan tare da ɗan sauyi kaɗan
---
1. A wannan hadisi, Imam Ali (A.S.) yana yin hasashen abin da zai faru nan gaba. Ya gaya wa mabiyansa cewa Mu'awiya ba zai mutu a wannan yaƙin ba, sai dai zai yi mulki a kan mutane. Saboda haka sahabbansa suka yi mamaki suka tambaye shi: "Idan ka san cewa zai rayu kuma zai karɓi mulki, to mene ne amfanin yaƙarsa yanzu?" Sai Imam ya amsa cewa aikinsa ba shi ne tabbatar da wani sakamako na musamman ba, amma aikinsa shi ne ya yi abin da yake daidai bisa gaskiya, ko da kuwa abin da zai faru a gaba ya bambanta.
Ra'ayinka