Alhamis 16 Yuli 2026 - 00:06
Silsilar Tattaunawa Kan Mahdawiyya (57) | Tawqi'o'in Imam Mahdi (A.F)

Hauza/ Daya daga cikin hanyoyin tantance al'amura da warware shubuhohi ita ce amfani da shawarwari da kuma amfana da tawqi'o'i da rubuce-rubucen da Imam Mahdi (A.F) yake aikawa ga amintattun mutane.

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito cewa, ana gabatar muku da jerin bahasosin Mahdawiyya mai taken "Zuwa Ga Al'umma Mai Manufa", da nufin yada koyarwa da ma'arifin da suka shafi Imam Mahdi (A.F).

Tawqi'o'in Imam Mahdi (A.S.)

Babu shakka, duniya ba ta taɓa zama babu hujjar Allah ba, kuma a kowane zamani akwai wani Ma'asumi a cikin mutane domin cika hujja da bayyana hukunce-hukuncen Allah da umarninsa.

A lokacin gaibar Imam Mahdi (A.S.), duk da cewa ba ya bayyana ga jama'a ta yadda za su san shi, amma alkhairai da albarkatunsa suna ci gaba da gangarowa ga mutane a koyaushe.

Daya daga cikin hanyoyin tantance al'amura da warware shubuhohi ita ce amfani da shiriyarsa da kuma tawqi'o'i da rubuce-rubucen da yake aikawa ga mutanen da ya amince da su.

Mene ne Tawqi'i?

A ma'anar harshe (Lugga), tawqi'i yana nufin rubutu a jikin takarda. A ma'anar da aka saba amfani da ita kuwa (Isdilahance), yana nufin umarni da wasiƙun halifofi da sarakuna da suke aikawa ga mutane. Amma a cikin littattafan malaman Shi'a, ana kiran wasiƙu da umarnin da suke fitowa daga Imam Mahdi (A.S.) zuwa ga mabiyansa a lokacin gaiba da suna tawqi'i, kuma wannan shi ne abin da ake nufi a nan.

Nau'ukan Tawqi'o'i

Ana iya raba tawqi'o'in Imam Mahdi (A.S.) gida biyu:

A) Tawqi'o'in zamanin Gaiba Karama (Ghaibat al-Sughra)

A wannan lokaci, tawqi'o'i suna fitowa ta hannun mataimakan Imam guda huɗu, wato Usman bn Sa'id, Muhammad bn Usman, Husain bn Ruh da Ali bn Muhammad Samuri.

Ana fitar da su ne domin amsa tambayoyi da warware shubuhohi. Babban manufarsu ita ce bayyana abin da ya wajaba ga mabiya Shi'a da kuma cetonsu daga ruɗani.

B) Tawqi'o'in zamanin Babbar Gaiba (Ghaibat al-Kubra)

A zamanin Babbar Gaiba, babu shakka alakar Shi'a da Imam tana ci gaba ta hanyar da ba kai tsaye ba. Daya daga cikin hanyoyin wannan alaka shi ne fitowar tawqi'o'i masu daraja zuwa ga manyan malaman Shi'a da zababbunsu.

A cikin tawqi'o'in wannan zamani akwai muhimman abubuwa guda biyu:

Ba a yarda a bayyana irin waɗannan tawqi'o'i sai idan akwai larura, kuma ba kowa ne zai iya samun bayaninsu ba.

Amsa shubuhohi, tantance matsayin mutane, nazarin al'amuran zamani da makamantansu suna daga cikin manyan batutuwan da suke ƙunshe da su.

Shin tawqi'o'in Imam Mahdi (A.S.) da hannunsa aka rubuta su?

Amsa ita ce ba za a iya cewa dukkan tawqi'o'in da hannun Imam aka rubuta su ba, haka kuma ba za a iya musanta cewa wasu daga cikinsu da hannunsa aka rubuta su ba.

Wasu malamai sun yi imanin cewa Imam da kansa ne yake rubuta wasu tawqi'o'in, har ma rubutunsa sananne ne a wajen manyan sahabbansa da malaman zamaninsa, kuma suna gane shi sosai.

Misali, Ishaq bn Ya'aqub ya ce: "Na roƙi Muhammad bn Usman al-Umari ya kai wasiƙata ga Imam, wadda na tambaye shi wasu matsaloli da suka rikice mini. Sai amsar ta zo da rubutun Maigidanmu Sahib al-Dar."(Bihar al-Anwar, j.51, sh.349)

Wato ya rubuta wasiƙa zuwa ga Imam Mahdi (A.S.), kuma amsar ta dawo da rubutun Imam da kansa.

Sai dai kuma, wasu shaidu suna nuna cewa ba duka tawqi'o'in da hannun Imam aka rubuta su ba.

Misali, Abun Nasr Hibatullah ya ce: "Tawqi'o'in Sahibul Amr (A.S.) suna fitowa ta hannun Usman bn Sa'id da ɗansa Muhammad bn Usman zuwa ga Shi'arsa da irin rubutun da ake amfani da shi tun zamanin Imam Hasan Askari (A.S.)." (Biharul Anwar, juzu'i na 51, shafi na 346)

Abubuwan da Tawqi'o'in suka ƙunsa

Maganganun Imam Mahdi (A.S.) a cikin tawqi'o'i suna ɗauke da fannoni daban-daban, daga cikinsu akwai:

1. Bayanin Babbar Gaiba da alamomin bayyanarsa

Imam ya rubuta wa Ali bn Muhammad Samuri cewa:

«فَقَدْ وَقَعَتِ الْغَیْبَةُ الثَّانِیَةُ فَلَا ظُهُورَ إِلَّا بَعْدَ إِذْنِ اللَّهِ عَزَّ وَ جَلَّ وَ ذَلِکَ بَعْدَ طُولِ الْأَمَدِ وَ قَسْوَةِ الْقُلُوبِ وَ امْتِلَاءِ الْأَرْضِ جَوْراً.»

"Hakika Babbar Gaiba ta fara. Kuma babu bayyanata sai da izinin Allah Madaukaki, bayan dogon lokaci, taurin zukata da kuma cikar duniya da zalunci." (Kamaluddin, juzu'i na 2, shafi na 516)

2. Cikakken saninsa game da halin mabiyansa

A cikin wata tawqi'i zuwa ga Shaikh Mufid ya ce:

«فَإِنَّا یُحِیطُ عِلْمُنَا بِأَنْبَائِکُمْ وَ لاَ یَعْزُبُ عَنَّا شَیْءٌ مِنْ أَخْبَارِکُمْ وَ مَعْرِفَتُنَا بِالزَّلَلِ اَلَّذِی أَصَابَکُمْ مُذْ جَنَحَ کَثِیرٌ مِنْکُمْ إِلَی مَا کَانَ اَلسَّلَفُ اَلصَّالِحُ ... إِنَّا غَیْرُ مُهْمِلِینَ لِمُرَاعَاتِکُمْ وَ لاَ نَاسِینَ لِذِکْرِکُمْ وَ لَوْ لاَ ذَلِکَ لَنَزَلَ بِکُمُ اَللَّأْوَاءُ وَ اِصْطَلَمَکُمُ اَلْأَعْدَاءُ فَاتَّقُوا اَللَّهَ جَلَّ جَلاَلُهُ.»

"Lallai muna da cikakken sani game da halin rayuwarku. Babu wani labarinku da yake ɓuya gare mu... Ba ma yin sakaci wajen kula da ku, kuma ba ma manta da ku. Da ba haka ba, musibu sun sauko muku kuma maƙiyanku sun hallaka ku. Saboda haka ku ji tsoron Allah."

(Biharul Anwar, juzu'i na 53, shafi na 174)

3. Karyata masu da'awar alaƙa ta musamman da Imam

Imam ya rubuta wa Ali bn Muhammad Samuri cewa:

«وَ سَیَأْتِی شِیعَتِی مَنْ یَدَّعِی اَلْمُشَاهَدَةَ أَلاَ فَمَنِ اِدَّعَی اَلْمُشَاهَدَةَ قَبْلَ خُرُوجِ اَلسُّفْیَانِیِّ وَ اَلصَّیْحَةِ فَهُوَ کَاذِبٌ مُفْتَرٍ.»

"Ba da daɗewa ba wasu za su zo suna ikirarin cewa sun gan ni. Ku sani, duk wanda ya yi wannan iƙirari kafin fitowar Sufyani da kuma kiran sama, to shi maƙaryaci ne kuma mai ƙirƙirar ƙarya." (Kamaluddin, juzu'i na 2, shafi na 516)

4. Kawar da shakku game da Imamai (A.S.)

Lokacin da wasu daga cikin Shi'a suka yi zaton cewa Imam Hasan Askari (A.S.) bai bar magaji ba, Imam Mahdi (A.S.) ya rubuta musu cewa:

«أنه أنهی إلی ارتیاب جماعة منکم فی الدین، وما دخلهم من الشک والحیرة فی ولاة أمرهم، فغمنا ذلک لکم لا لنا، وساءنا فیکم لا فینا، لأن الله معنا.»

"An isar mini da cewa wasu daga cikinku sun shiga shakku da ruɗani game da addininsu da Imaminsu. Wannan ya ba mu baƙin ciki saboda ku, ba saboda kanmu ba. Allah yana tare da mu." (Al-Ihtijaj, juzu'i na 2, shafi na 278)

5. Yabon manyan mabiyan Shi'a

A cikin tawqi'i zuwa ga Sheikh Mufid, Imam ya rubuta:

«لِلْأَخِ اَلسَّدِیدِ وَ اَلْوَلِیِّ اَلرَّشِیدِ اَلشَّیْخِ اَلْمُفِیدِ ... سَلاَمٌ عَلَیْکَ أَیُّهَا اَلْوَلِیُّ اَلْمُخْلِصُ فِی اَلدِّینِ اَلْمَخْصُوصُ فِینَا بِالْیَقِینِ... .»

"Ga ɗan'uwa nagari kuma waliyyi shiryayye, Sheikh Mufid... Aminci ya tabbata a gare ka, ya kai waliyyi mai ikhlasi a addini, wanda aka kebance shi da cikakken yaƙini game da mu." (Al-Ihtijaj, juzu'i na 2, shafi na 495)

6. Koyar da addu'a da yadda ake tawassuli

An ruwaito cewa Abdullah bn Ja'afar Humairi ya tambayi Imam yadda ake tawassuli da shi. Sai Imam ya rubuta cewa:

«...بعد صلاة اثنتی عشرة رکعة تقرأ قل هو الله أحد فی جمیعها رکعتین رکعتین ثم تصلی علی محمد وآله ، وتقول قول الله جل اسمه: سلام علی آل یاسین...

"Bayan raka'a goma sha biyu na salla (salloli shida, raka'a biyu-biyu), a karanta Suratul Ikhlas a kowace raka'a, sannan a yi salati ga Annabi (S.A.W.A.) da iyalansa, sannan a karanta abin da Allah Ya ce: "Salamun Ala Ali Yasin..." (Biharul Anwar, juzu'i na 53, shafi na 174)

Wannan addu'a ita ce ake kira Ziyarar Aal Yasin.

7. Umarni da yawaita addu'ar gaggauta bayyanarsa

A cikin wata tawqi'i zuwa ga Ishaq bn Ya'aqub, Imam ya ce:

«إِنِّی لَأَمَانٌ لِأَهْلِ اَلْأَرْضِ کَمَا أَنَّ اَلنُّجُومَ أَمَانٌ لِأَهْلِ اَلسَّمَاءِ فَأَغْلِقُوا بَابَ اَلسُّؤَالِ عَمَّا لاَ یَعْنِیکُمْ وَ لاَ تَتَکَلَّفُوا عِلْمَ مَا قَدْ کُفِیتُمْ وَ أَکْثِرُوا اَلدُّعَاءَ بِتَعْجِیلِ اَلْفَرَجِ فَإِنَّ ذَلِکَ فَرَجُکُمْ.» 

"Ni amincin mutanen duniya ne, kamar yadda taurari suke amincin mazaunan sama. Don haka ku guji tambayar abin da ba ya amfanar ku, kada kuma ku wahalar da kanku da neman sanin abin da ba a ɗora muku ba. Kuma ku yawaita yin addu'ar Allah Ya gaggauta bayyanata, domin hakan shi ne samun kuɓutarku." (Kamaluddin, juzu'i na 2, shafi na 483)

Baya ga haka, tawqi'o'in suna ƙunshe da karyata masu bidi'a da masu adawa, amsa shubuhohi da tambayoyin fikihu, shawartar mutane da su ji tsoron Allah, karfafa soyayyar Ahlul Baiti (A.S.), da sauran muhimman koyarwa.

Wannan tattaunawa za ta ci gaba...

An ciro daga maƙalar "Mahiyyar Tawqi'o'in Imam Mahdi (A.S.)", wadda Ghulam Ridha Salihi ya rubuta, tare da ɗan gyara kaɗan

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha