Talata 30 Yuni 2026 - 19:04
Darasin Akhlaƙ | Sirrin Zubar Hawaye Da Shahidin Jagora Ya Bayyana Daga Wasiyyar Annabi (S.A.W.A)

Hauza/ Shahidin jagora, a lokacin da yake yin bayani kan wasiyyar Annabi (S.A.W.A) ga Amirul Muminina (A.S) game da muhimmancin yin kuka saboda tsoron Allah, ya bayyana kuka a matsayin sakamakon sauye-sauye na cikin gida da kuma fahimtar gaskiya; ta yadda kuka ba tare da wannan yanayi na cikin zuciya ba, ba shi da wani amfani.

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito cewa, Hazrat Ayatullah Imam Khamenei (Allah ya tsarkake kyakkyawan ruhinsa) a buɗe wani darasin karatun Bahsul Kharij, ya yi bayani kan wani hadisi na tarbiyya. "Yin kuka saboda tsoron Ubangiji" shi ne ma'anar bayanin wannan hadisi na akhlak daga fiyayyen halitta Annabin Musulunci Hazrat Muhammad Mustafa (S.A.W.A). Ga dai fassarar rubutaccen jawabin na Shahidin jagoran kamar haka:

Bismillahir Rahmanir Rahim

Alhamdu lillahi Rabbil Alamin

Abu na hudu; daga cikin wasiyyar da Annabi Mai Daraja (S.A.W.A) ya yi wa Amirul Muminina (A.S); sashi na hudu shi ne: «کثره البکاء من خشیه اللّه تعالی» (Yawaita kuka saboda tsoron Allah Maɗaukakin Sarki). Yawaita kuka daga tsoron Ubangiji.

Hakikanin Kuka da Yanayin Zuciya

Yin kuka wani yanayi ne a cikin dan adam wanda ke kasancewa sakamakon wasu abubuwa da sauye-sauye na zuciya. Yin kuka na dole ko na tursasawa, ko dai ba zai yiwu ba, ko kuma idan ma muka kaddara cewa ya yiwu amma bai samo asali daga sauye-sauyen cikin zuciya ba, to wannan kukan ba shi da wani amfani.

Wancan kukan da yake da amfani shi ne wanda ya samo asali daga hango wata gaskiya; wanda mafi muhimmanci daga cikin wadannan gaskiyoyi shi ne mutum ya ji kansa a gaban Allah Maɗaukakin Sarki, kuma sakamakon girman Ubangiji da daukakarsa, sai wani yanayi na kaskantar da kai, tsoro, da mika wuya ya bayyana a cikinsa, wanda zai yi sanadin kwararar hawayensa. Wannan yanayi na juyawar zuciya a cikin mutum wanda ke sanya hawaye su kwarara; shi ne abin da ya kamata mutum ya samar a ransa.

Hanyar Samun Wannan Yanayi

Hanyar samun hakan ita ce juyo da hankali ga Allah Maɗaukakin Sarki. A cikin sallah, a cikin addu'a, idan har mutum ya ji cewa yana tsaye ne a gaban Allah Maɗaukakin Sarki, wannan jin cewa yana gaban Ubangiji da kansa yana sauya mutum. Yana sanya hawaye su kwarara.

Wannan shi ne sirri da amfanin halartar da zuciya a cikin salla (Hudurul Qalb). Tabbas, halartar zuciya ba wai kawai mutum ya rika fassara kalmomin salla a cikin kansa ba ne. A'a, a gaskiya ya ji cewa yana gaban Ubangiji kuma yana magana da Allah Maɗaukakin Sarki; wannan jin ne ke samar da yanayin tsoron Allah (khushu'i) a cikin mutum, kuma wannan yanayi na khushu'i yana kaiwa ga yin kuka. Mafi yawancin lokuta, haka abin yake.

Shawarar Manyan Malamai Kan Sallah 

Manyan malamai na da sun kasance suna ba da shawarar cewa: "Abin da yake da muhimmanci shi ne ku kula kada ku fita daga cikin salla da gangan (wato kin mayar da hankali)." Ma'ana, kada ku tafiyar da hankalinku zuwa wani wuri da gangan.

Wani lokacin mutum yana cikin sallah sai hankalinsa ya fita ta dabi'ance, wanda mafi yawan lokuta wannan ba ya faruwa da zabinsa. Tabbas, idan mutum zai iya hana rarrabuwar hankalinsa a cikin sauran sa'o'i na dare da rana, kuma ya kasance mai ambaton Allah da tunawa da Shi; wannan yanayi na ambaton Allah a cikin sallah zai fi sauƙi ya samu gare shi. Amma a dabi'ance, idan muna cikin sallah, shagala ko dauke hankali daga sallah da kuma rashin mayar da hankali ga Allah yana faruwa da mu.

To, da zaran mun lura cewa hankalinmu ya shagala, sai mu dawo da hankalinmu nan da nan zuwa ga kasancewa a gaban Allah. Wannan shi ne abin da ake bukata, wanda manyan malamai suka kasance suna ba mu shawara mu da mutane irinmu.

Ko ta yaya dai, idan har wannan yanayi na mayar da hankali ya samu; to a bayansa akwai wannan kukan shi ma. Wannan kuka abu ne na dole (da zai biyo baya) wanda ke fitowa daga wancan tsoron Allah, kuma a dabi'ance yake samun mutum.

Wassalamu Alaikum wa Rahmatullah.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha