Asabar 27 Yuni 2026 - 19:35
Silsilar Tattaunawa Kan Mahdawiyya (46) | Matsayi Da Darajar Masu Jiran Bayyanar Imam Mahdi (A.F) Na Gaskiya

Hauza/ Sakamakon keɓantattun yanayi da ke mulkar mutanen zamanin jiran bayyanar Imam, idan har suka kasance masu jiran gaskiya, za su sami matsayi da daraja mai kima sosai.

Bisa rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, ana gabatar da jerin bahasin Mahdawiyya mai taken "Zuwa Ga Al'umma Mai Manufa", da nufin yaɗa koyarwa da ilimin da ke da alaƙa da Imamin Zamani (Allah Ya gaggauta bayyanarsa) ga ku masana masu daraja.

A cikin koyarwa mai daraja ta Ma'asumai (A.S), an ambaci matsayi da daraja ga masu jiran gaskiya na Iman Mahdi (A.F) ta yadda abin yake da ban mamaki da ban al'ajabi kwarai, wanda hakan ke sanya wannan tambayar cewa: Ta yaya zai kasance wannan yanayin ya zama yana da irin wannan babbar kima?

Yanzu za mu yi nuni da wasu daga cikin falaloli da darajojin masu jiran bayyanar Imam (Muntazirun) ta hanyar amfani da hadisan Ma'asumai (A.S):

Mafi Alherin Mutane

Sakamakon keɓantattun yanayi da ke mulkar mutanen zamanin jiran bayyanar Imam, idan har suka kasance masu jiran gaskiya, za su sami matsayi mai kima sosai.

Imam Sajjad (A.S) yana cewa game da wannan:

«إِنَّ أَهْلَ زَمَانِ غَیْبَتِهِ وَ الْقَائِلِینَ بِإِمَامَتِهِ وَ الْمُنْتَظِرِینَ لِظُهُورِهِ... أَفْضَلُ مِنْ أَهْلِ کُلِّ زَمَان لِأَنَّ اللَّهَ تَعَالَی ذِکْرُهُ أَعْطَاهُمْ مِنَ الْعُقُولِ وَ الْأَفْهَامِ وَ الْمَعْرِفَةِ مَا صَارَتْ بِهِ الْغَیْبَةُ عَنْهُمْ بِمَنْزِلَةِ الْمُشَاهَدَةِ».

"Mutanen zamanin gaibar wannan Imam ɗin waɗanda suka yi imani da shugabancinsa (Imamancinsa) kuma suke jiran bayyanarsa, sun fi mutanen kowane zamani alheri; domin Allah Maɗaukakin Sarki Ya ba su hankali, fahimta, da ilimi da ya sanya ɓoyuwar Imam a gare su ta kasance kamar suna ganinsa da idanunsu." (Kamaluddin wa Tamamun Ni'imah, juzu'i na 1, shafi na 319)

Masu Kasancewa a Cikin Tantinsa Lokacin Bayyana

Daga cikin mafi girman buri na dukkan mutanen kirki na duniya shi ne kasancewa a zamanin da babu wata barna, zalunci, da halaka a cikinsa. Wannan falala tana cika ne lokacin da mutum ya kasance a mafi kusa da shugaban juyin juya hali a lokacin bayyanarsa, wato a matsayin kwamanda a cikin tantinsa.

Imam Sadik (A.S) yayin siffanta masu jiran gaskiya waɗanda ba su riski zamanin bayyanar ba, yana cewa:

«مَنْ مَاتَ مِنْکُمُ عَلی هَذا الْاَمْرِ مُنتَظِراً کانَ کَمَنْ هُوَ فِی الفُسْطَاطِا الَّذِی لِلْقائم.»

"Duk wanda ya mutu daga cikinku alhalin yana jiran wannan al'amari (bayyanar Imam), yana da matsayi kamar wanda yake a cikin tantin Al-Qa'im (Imam Mahdi). (Al-Kafi, juzu'i na 5, shafi na 22)

Ladansu Kamar Ladan Mai Sallah da Azumi Ne

Daga cikin mafi daukakar ayyukan ibada akwai sallah da azumi. Daga hadisai an fahimci cewa idan mutum ya gudanar da rayuwarsa yana jiran bayyanar Imam, kamar yana cikin ibadar sallah da azumi ne.

Imam Baƙir (A.S) yana cewa game da wannan:

«وَاعْلَمُوا اَنَّ المُنتَظِرَ لِهذا الاَمْرِ لَهُ مِثْلُ اَجْرِ الصَّائِمِ القائِمِ.»

"Ku sani cewa, lallai ladan mai jiran wannan al'amari yana da misalin ladan mai azumi (da rana) da mai tsayuwar dare (da sallah)." (Al-Kafi, juzu'i na 2, shafi na 222)

Mafi Darajar Al'umma kuma Abokin Manzo (S.A.W.W)

A cikin mutane, wanene ya fi daraja fiye da Manzon Musulunci mai daraja (S.A.W.A) wanda shi ne mafi darajar Annabawan Allah kuma mafi soyuwar halitta a wurin Allah? To, wanda ya rayu a zamanin jiran bayyanar Imam kamar yadda ya dace, zai kasance mafi darajar mutum daga al'ummar Annabi kuma a kusa da wannan babban mutum, kamar yadda Annabi (S.A.W.A) da kansa ya ce:

«... اُولئِکَ رُفَقائی وَاکْرَمُ اُمَّتی عَلَی.»

"Waɗancan sune abokaina, kuma mafi darajar al'ummata a gare ni. (Kamaluddin wa Tamamun Ni'imah, juzu'i na 1, shafi na 286)

Masu Yaki a Tafarkin Allah Tare da Manzo (S.A.W.A)

Daga cikin mafi darajar mutane akwai masu jihadi a tafarkin Allah. Wannan falala tana cika ne lokacin da wannan jihadin ya kasance tare da Cikakken Mutum kuma Manzon Musulunci mai daraja (S.A.W.W).

Imam Husaini (A.S) yana cewa:

«إِنَّ الصَّابِرَ فِی غَیْبَتِهِ عَلَی الْأَذَی وَ التَّکْذِیبِ بِمَنْزِلَةِ الْمُجَاهِدِ بِالسَّیْفِ بَیْنَ یَدَیْ رَسُولِ اللَّهِ ص‌.»

"Wanda ya yi haƙuri a lokacin ɓoyuwarsa (Imam) akan cutarwa da ƙaryatawa, yana da matsayin mai jihadi da takobi a gaban Manzon Allah (S.A.W.A)." (Uyun Akhbar al-Rida, juzu'i na 1, shafi na 68)

Suna da Ladan Shuhada Dubu na Farkon Musulunci

Game da daukakar masu jiran gaskiya da masu juriya akan soyayya da biyayya ga Ahlul-Baiti (A.S), an yi magana akan ladan da ya kai na shuhada dubu daga cikin shuhadan yakin Badar da Uhud na farkon Musulunci.

Imam Sajjad (A.S) yana cewa game da wannan:

«مَن ثَبَتَ عَلی مُوالاتِنا فِی غَیْبَةِ قائِمِنا اَعْطاهُ اللَّهُ عَزَّوَجَلَّ اَجْرَ اَلْفَ شَهیدٍ مِنْ شُهَداءِ بَدْرٍ وَاُحُدٍ.»

"Duk wanda ya kasance tsayayye akan soyayyarmu a lokacin ɓoyuwar Al-Qa'im ɗinmu, Allah Maɗaukakin Sarki zai ba shi ladan shuhada dubu daga cikin shuhadan Badar da Uhud." (Kamaluddin wa Tamamun Ni'imah, juzu'i na 1, shafi na 323)

Wannan tattaunawa za ta ci gaba...

An ɗauko ne daga littafin "Darsnameh Mahdaviyyat; na Khodamurad Salimiyan", tare da ɗan gyara kadan

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha