Jummaʼa 26 Yuni 2026 - 14:28
Mun Rugurguza Shirin Haɗin Gwiwa Tsakanin Isra'ila Da Amurka, Kuma Makiyi Ba Shi Da Wata Mafita Face Janyewa

Hauza/ Babban Sakataren ƙungiyar Hizbullah ta Lebanon, Sheikh Na'im Qasim, ya bayyana a lokacin jawabin ranar Ashura cewa, dakarun gwagwarmaya sun yi nasarar rugurguza manufofin haɗin gwiwar Amurka da Isra'ila, inda ya jaddada cewa makiyi ba shi da wani zaɓi da ya rage masa face ya janye dakarunsa cikin tawaya da kasakanci.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Sheikh Na'im Qasim ya bayyana hakan ne yayin babban jawabin da ya gabatar na tunawa da ranar 10 ga watan Muharram (Ashura), inda ya ce: "A Ashurar wannan zamani, muna tsaye kafada da kafada da tunanin Imam Khumaini, Imam Khamenei, Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamenei, Imam Musa Sadr, Sheikh Raghib Harb, Sayyid Abbas Musawi, Sayyid Hassan Nasrallah, Sayyid Hashim Safiyuddin, da daukacin majahidai, shahidai, masu rauni, fursunoni, da iyalansu."

Ma'anar Ashura Da Ci Gaban Gwagwarmaya 

Babban Sakataren na Hizbullah ya bayyana cewa Ashura ita ce nasarar jini a kan takobi, inda jinin Imam Hussain (A.S) yake rura wutar 'yanci, yayin da muryar Sayyidah Zainab (S.A) ke zama abin koyi ga masu fafutukar jihadi.

Ya ƙara da cewa, duk da irin wahahalun da mutanen Lebanon suka fuskanta na hijira, kora ta tilas, jin zafi, da rashi, taron Ashura na bana ya shaida gagarumin taron jama'a a kowane sashi, wanda hakan ke nuna cewa al'umma ce ta Hussaini wadda ta koyi darasin juriya daga Karbala.

Rugurguza Manufofin Amurka Da Isra'ila A Lebanon Da Iran

Sheikh Na'im Qasim ya yi tsokaci kan hare-haren wuce gona da iri da yahudawan sahyoniyya da Amurka suka kai wa Lebanon ta kasa, teku, da sama, inda ya ce makasudin hare-haren shi ne murkushe baki daya kungiyar Hizbullah da mutanen da ke goyon bayanta domin mamaye kasar baki daya a cikin shirin "Isra'ila Babba". "Amma da taimakon Allah, da kuma tsayuwar daka irin ta Karbala ta dukkan mutanenmu mazauna kwarai da 'yantattu, mun yi nasarar dakatar da wannan mamaya kuma mun sami babban rabo. Muna shelar cewa: Mun rugurguza shirin Isra'ila da Amurka kuma mun shiga sabon zamani," in ji Sheikh Qasim. 

Ya kuma bayyana cewa wannan makarkashiya ta faru ne a lokaci guda da aka kai wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran hari domin hambarar da kasarta da kwashe arzikinta. Sai dai muƙawamar Iran a karkashin jagorancin Imam Khamenei ta kai su ga samun nasara da kuma tattaunawa ta yarjejeniya, wadda ke nuna amincewa a hukumance ga lallasar da Amurka da Isra'ila suka sha.

Sharuɗɗa guda 5 Na Tabbatar Da 'Yancin Kasar

Babban Sakataren na Hizbullah ya shimfida sharuɗɗa guda biyar (5) masu muhimmanci:

 1. Janyewar Isra'ila Ba Tare Da Sharaɗi Ba: Isra'ila ba ta da wani zaɓi face ta janye gaba ɗaya daga kowane sashi na ƙasar Lebanon, musamman a kudancin kogin Litani, ba tare da gindaya wa huldar ƙasar kowane irin tarnaki ba.

 2. Dorewar Gwagwarmaya: Ƙungiyar gwagwarmaya (Muƙawama) za ta ci gaba da kasancewa da dukkan ƙarfinta a matsayin ginshikin 'yancin kai da tsaron Lebanon.

 3. Haɗin Kan Siyasa Na Cikin Gida: Dole ne shugabannin siyasa su hada kai su daina bin umurnin kasashen waje (Amurka da Isra'ila), kuma su mayar da hankali wajen gyaran tattalin arziki da taimakon al'umma.

 4. Amfana Daga Dangantakar Iran: Dole ne a yi amfani da nasarorin da Iran ta samu wajen karfafa tsaron Lebanon, domin Iran ta tabbatar da cewa ita ce hanyar ceto.

 5. Kore Kutsen Kasashen Waje Masu Goyon Bayan Sahyoniyya: Dole ne a katse hannun kasashen da ke matsa lamba domin a ajiye makamai ko yin sulhu da Isra'ila, a maimakon haka a karɓi ƙasashen da ke taimakon sojin Lebanon don korar mamaya.

Jinjina Ga Al'ummar Palasɗinu, Yaman, Da Iraƙi

A ƙarshe, Sheikh Na'im Qasim ya aike da gaisuwa ta girmamawa ga jaruman mutanen Gaza da Palasɗinu, yana mai cewa jinin shuhadansu shi ne jigon 'yanci na duniya, kuma Palasɗinu za ta ci gaba da zama matattarar gwagwarmayarsu.

Haka nan ya jinjina wa jajirtattun mutanen Yaman da dakarunsu na soja a ƙarƙashin jagorancinsu na gari, waɗanda suka tsaya tsayin daka tare da Palasɗinu da Lebanon lokacin da duniya ta yi shiru. Ya kuma mika godiya ga al'ummar Iraƙi, manyan maraji'an addini, dakarun Hashdus Sha'abi, da gwamnatin ƙasar saboda goyon baya da taimako na har abada da suka ba su.

Jawabin ya kammala da jaddada taken juriya na "Haihat minnaz Zillah".

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha