A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Hujjatul Islam wal Muslimin Jawaheri, wakilin Ayatullah Shubairi Zanjani, ya amsa wata tambaya game da hukuncin shari'a na tsarkakar kujera mai najasa ta hanyar hasken rana.
Tambaya: Idan muka sanya kujera mai najasa a gaban hasken rana kai-tsaye, shin ana daukarta a matsayin mai tsarki ko a'a?
Amsa: Hujjatul Islam wal Muslimin Jawaheri, a bisa fatawar Hazrat Ayatullah Shubairi Zanjani, ya bayyana cewa: Idan kujera ta najastu da najasa, ba za ta taba tsarkaka ba ta hanyar sanya ta a gaban hasken rana. Hasken rana yana tsarkake abubuwan da ke jikin gine-gine da kuma abubuwan da ke kafe (waɗanda ba sa tashi daga gurbinsu) kawai; wato ana amfani da shi ne wajen tsarkake gini.
Amma game da kujeru, kafet (tabarmu/katifu) da makamantansu, hasken rana ba ya zama sanadin tsarkakarsu.
Ra'ayinka