Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito, Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah Sayyid Mujtaba Hussaini Khamenei ya fitar da saƙo dangane da Ranar Ma’aikata da Ranar Malamai.
Ga cikakken rubutun saƙon kamar haka:
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai
Ranakun goma sha ɗaya da goma sha biyu ga watan Ordibehesht ranaku ne da ake girmama matsayin ma’aikata da darajar malamai. Baya ga yabon baki da na alama, wanda shi ma a nasa bangaren aiki ne mai dacewa kuma daidai, cigaban kowace ƙasa yana jingina ne ga fikafikai biyu: ilimi da aiki.
Malami shi ne ke taka rawa a mataki na farko wajen tabbatar da wannan buri. Nauyin koyar da ilimi, ƙara ƙwarewa, da wani muhimmin ɓangare na bunƙasa fahimta da gina asalin halayen tsara (tsatso) ta gaba yana kan wuyansa. Dalibai na makarantu, na jami’o’i da na Hauza waɗanda ke girma tare da kowane malami, a nan gaba ba mai nisa ba za su yi amfani da ƙwarewar da suka koya da ilimin da suka samu, kuma mai yiyuwa ne a halayensu, mu’amalarsu da maganganunsu a fannoni daban-daban na rayuwa—tun daga dumin majalisar iyali har zuwa wurin aiki da kuma kan tituna—su zama kamar madubi da ke nuna halaye da maganganun malamansu.
A gefe guda kuma, fagen aiki wani fili ne mai faɗi da girman ƙasa gaba ɗaya, wanda ya fara daga cikin gidaje, ofisoshi, wuraren kasuwanci da masallatai har zuwa gonaki, asibitoci, masana’antu, ma’adinai da nau’o’i masu yawa na ayyukan hidima. Duk yadda wannan fili mai faɗi ya fi cin gajiyar abubuwa biyu wato ƙwazo da sadaukarwa—waɗanda suke daga cikin ginshiƙan kowace babbar nasara—haka kuma cigaban ƙasa zai fi tabbata da kyau.
Mun san cewa wani ma’aikaci a ƙarƙashin sadaukarwa da kyakkyawan aiki wani lokaci yana kaiwa wani matsayi mai girma har ya cancanci, kamar yadda ake sumbatar hannu mai cike da tausayin malami da mai tarbiyya, a sumbaci hannunsa mai ƙarfi da ƙwarewa da nufin godiya da girmamawa. Wannan kuwa abu ne da tushensa yake fitowa daga tarbiyyar farko ta kowane mutum wato iyayensa, sannan daga fahimtar zama a gaban malami.
Yanzu da Jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan fiye da shekaru arba’in da bakwai na gwagwarmaya, tare da dogaro ga falalar Allah, a fagen yaƙin soja da makiyan cigaba da bunƙasar ta ta sami damar nuna wani ɓangare na ƙarfinta mai ban mamaki ga duniya, dole ne a matakin jihadin tattalin arziƙi da na al’adu ma ta sa su yanke ƙauna tare da shan kaye.
Malamai su ne mafi tasiri a gwagwarmayar al’adu, kuma ma’aikata na daga cikin mafi tasiri a gwagwarmayar tattalin arziƙi; har ma ana iya cewa su ne ƙashin bayan fagen al’adu da tattalin arziƙi. Saboda haka ya zama dole su fahimci muhimmancin matsayinsu na musamman da ya fi kawai aiki wanda ake karɓar albashi a kansa.
Haka kuma ya kamata a kula cewa yabon baki na shekara‑shekara ko na lokaci‑lokaci, ko da yake yana da kyau kuma ya dace, amma godiya ga ƙoƙarin waɗannan rukuni biyu dole ne ta fi wannan zurfi kuma ta zama a aikace. Ina ganin kamar yadda al’umma mai daraja ta Iran ke fitowa fili da kan tituna domin nuna goyon baya ga sojojin ƙasar su, haka ma ya dace su nuna goyon baya mai ƙarfi wajen taimakon malamai da ma’aikata.
Daga cikin wannan ya kamata a ƙara samar da haɗin kai tsakanin iyalan dalibai da daliban jami’a wajen tafiyar da makarantu da jami’o’i fiye da da, haka kuma a tallafa wa ma’aikata masu samar da kayayyaki ta hanyar fifita amfani da kayayyakin da aka ƙera a cikin ƙasa. Musamman ma masu kasuwancin da suka fuskanci matsaloli su yi ƙoƙari gwargwadon iko su guji rage ma’aikata ko sallamar su, ko a bangaren masana’antu ko kuma na ayyukan hidima, kuma ma su ɗauki kowane ma’aikaci a matsayin wata dukiya ta wannan cibiyar samarwa ko hidima; kuma tabbas gwamnati mai girma ma ta tallafa da gwargwadon ikon ta ga wannan aiki na alheri.
Iran mai daraja, kamar yadda bayan shekaru na ƙoƙari ta bayyana a matsayin wata ƙarfi ta soja, insha Allahu kuma da falalar Allah, ta hanyar tsara layukan asalin Iran‑Musulma da kuma zurfafa su cikin tunani da zukatan matasan ƙasar nan ta hannun masu tarbiyya da malamai, da kuma fifita amfani da kayayyakin da aka samar a cikin ƙasa wanda shi ne sakamakon ƙoƙarin ma’aikatan Iran masu wahala, za ta bi hanyar wucewa zuwa kololuwar cigaba da bunƙasa. Kuma wannan, da addu’ar alheri da taimakon shugabanmu (Allah Ya gaggauta bayyanarsa), zai faru cikin sauri da kuma yanayi mafi kyau, da izinin Allah Maɗaukaki.
Wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Sayyid Mujtaba Hussaini Khamenei
11 / Ordibehesht / 1405 (01/ Mayu/2026)
Ra'ayinka