Alhamis 17 Satumba 2026 - 13:45
Fahimtar Addini Mai Zurfi da Yaɗa Addini Su Ne Manyan Manufofin Ɗaliban Hauza

Hauza/ Hujjatul Islam wal Muslimin Muhsin Qara’ati ya bayyana cewa tafaƙƙuhu (zuzzurfan sanin Addini) a cikin addini da yaɗa koyarwar addinin Allah su ne manyan ayyukan da ya kamata ɗaliban makarantun Hauza su mayar da hankali a kai, yana mai jaddada cewa manufar Hauza ita ce tarbiyyar malamai nagari masu zurfin ilimi da hidima ga addini.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, a yayin bikin buɗe darussan Cibiyar Ilimi ta Hauzar Imam Mahdi (A.S.) da ke birnin Qum, Hujjatul Islam Qara’ati ya ce ɗaliban Hauza suna da muhimmiyar rawa wajen samar da ilimi, yaɗa ilimin addini da kuma aiwatar da abin da suka koya a rayuwarsu.

Ya bayyana cewa ko da ɗalibi bai kai matakin ijtihadi da rubuta ayyukan ilimi ba, zai iya taka muhimmiyar rawa wajen yaɗa koyarwar Alƙur’ani da Ahlulbaiti (A.S.) ta hanyar rubutu, magana da wa’azi.

Hujjatul Islam Qara’ati ya jaddada cewa samun ilimin addini bai kamata ya tsaya ga karatu kawai ba, sai an mayar da shi aiki da kyawawan halaye. Ya kuma yi kira ga ɗaliban Hauza da kada su ji tsoron kowa face Allah wajen gudanar da aikin wa’azi da hidimar addini.

A wani ɓangare na jawabinsa, ya bayyana cewa daga cikin manyan manufofin kafa makarantun Hauza akwai horar da malamai da za su iya amsa tambayoyi da shubuhohin da ake gabatarwa game da addini, ta hanyar ilimi da hujjoji masu gamsarwa.

Ya kuma yi gargaɗi da kada ɗalibai su ɗauki samun takardar shaidar karatu a matsayin babban manufar karatunsu, yana mai cewa: “A karɓi takardar shaidar karatu, amma kada a yi karatu saboda takardar shaidar.” A cewarsa, takarda ta zama wata hanya ta taimaka wa ɗalibi wajen cimma burinsa na neman ilimi da hidima ga addini da al’umma.

A ƙarshe, Malam Qara’ati ya yi kira ga ɗaliban Hauza da su riƙa ɗaukar karatunsu da muhimmanci, su ci gaba da neman ilimi a kowane lokaci, tare da amfani da lokutan hutu wajen karatu, bincike da rubuce-rubucen ilimi, domin cimma manufar tarbiyyar malami nagari mai alaƙa da Alƙur’ani da koyarwar Allah.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha