Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito cewa buƙatar al'umma ga gwamnati tana daga cikin muhimman abubuwan da rayuwar ɗan Adam ba za ta iya gudana ba tare da su ba. Alƙur'ani mai girma ya ba da labarin cewa Annabawan Allah sun kafa gwamnatoci. Daga cikinsu akwai:
Game da zuriyar Annabi Ibrahim (A.S.):
﴿فَقَدْ آتَیْنَا آلَ إِبْرَاهِیمَ الْکِتَابَ وَالْحِکْمَةَ وَآتَیْنَاهُمْ مُلْکًا عَظِیمًا﴾
"Lalle ne Mun bai wa zuriyar Ibrahim Littafi da Hikima, kuma Mun ba su mulki mai girma." (Suratun Nisa'i: 54).
Game da Annabi Dawud (A.S.):
﴿وَآتَاهُ اللَّهُ الْمُلْکَ وَالْحِکْمَةَ}
"Allah Ya ba shi mulki da hikima." (Suratul Baƙara: 251).
Game da Annabi Sulaiman (A.S.):
{وَهَبْ لِی مُلْکًا}
"Ya Ubangijina! Ka ba ni mulki..." (Suratu Sad: 35–36).
Game da Annabi Yusuf (A.S.):
﴿وَکَذَلِکَ مَکَّنَّا لِیُوسُفَ فِی الْأَرْضِ﴾
"Haka kuma Muka tabbatar wa Yusuf matsayi a cikin ƙasa." (Suratu Yusuf: 56).
Game da Dalut:
﴿إِنَّ اللَّهَ قَدْ بَعَثَ لَکُمْ طَالُوتَ مَلِکًا﴾
"Lalle Allah Ya naɗa muku Dalut a matsayin sarki." (Suratul Baƙara: 247).
Manzon Allah (SAWA), wanda shi ne abin koyi mafi kyau, bayan hijirarsa zuwa Yathrib (Madina), ya kafa gwamnati. Wannan lamari abin da Shi'a da Ahlus-Sunnah suka yi ittifaki a kansa ne. Sai dai Ahlus-Sunnah suna kallon al'amarin halifanci a matsayin abin da mutane suke tsarawa, kuma suna bin ka'idar halifanci wadda ta ci gaba ta matakai uku:
1. Halifancin Banu Umayya har zuwa shekara ta 132H.
2. Halifancin Banu Abbas har zuwa shekara ta 656H.
3. Sannan Halifancin Usmaniyya har zuwa shekara ta 1924 Miladiyya.
A mahangar Shi'a kuwa, ka'idar ita ce Imama. Mataki na farko na Imama, wato Imama ta asali (Imamah bil-Asalah), ta ci gaba har zuwa shekara ta 260H, kuma Imaman Shi'a sun kasance masu da'awar haƙƙin shugabanci. Bayan haka sai mataki na biyu wanda ake kira Imama ta wakilci (Imamah bin-Niyabah).
Manufar gwamnati ita ce aiwatar da addinin Musulunci, musamman bangarorin zamantakewa da rayuwar jama'a. Babban ɓangare na dokokin Musulunci dokoki ne na siyasa da zamantakewa, waɗanda ba za su tabbata ba sai an kafa gwamnatin Musulunci.
Waɗannan dokoki da hukunce-hukuncen Allah na dindindin ne, ba su takaitu ga zamanin da Imami Ma'asumi yake a fili ba. A lokacin gaiba ma wajibi ne a aiwatar da su.
Saboda haka, duk wani mutum ko wata ƙungiya da ta yi mulki ba ta hanyar Imama ta asali ko Imama ta wakilci ba, bisa ga nassoshin Shi'a, ana ɗaukarta Ɗagutu.
Saboda haka, daga cikin nassoshin addini ana iya fahimtar waɗannan abubuwa:
Na Farko
Kafa gwamnati bayan wafatin Manzon Allah (SAWA) da kuma a zamanin gaibar Imam Mahdi (A.F.) a mahangar Shi'a batu ne na ilimin Kalam da Fikihu. Domin gwamnati tana daga cikin muƙaman Imama.
Manyan malaman Shi'a a lokacin gaiba sun yi imanin cewa haƙƙin shugabanci ya keɓanta ga malamai masu cikakken sharadi (Fuqaha), kuma sun bayyana hakan da sunan wakilcin malamai. Daga cikinsu akwai:
Sheikh Mufid, Abus-Salah al-Halabi, Ibn Idris, Shahidus Thani, Muhaqqiq Karaki, Naraqi, Sahibul Jawahir, da sauran manyan malamai.
A wannan zamani ne aka samu damar aiwatar da wannan tunani, inda Imam Khumaini (Q.S.) ya kafa gwamnatin Musulunci.
A yayin da Ahlus-Sunnah suke kallon kafa gwamnati a matsayin batu na fikihu kuma wajibi ne a yi ta.
(Za a ci gaba da Kashi na 2...)
Ra'ayinka