Asabar 4 Yuli 2026 - 20:01
Ramuwar Gayyar Allah Kan Amurka Da Gwamnatin Sahyoniya A Kurkusa Take

Hauza / Rundunar sojin ruwa ta dakarun kare juyin juya hali (IRGC) ta sanar da cewa: Ramuwar gayyar Allah kan Amurka 'yar ta'adda da kuma gwamnatin sahyoniya mara tushe, babu nisa.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran  Hauza daga Tehran, Rear Admiral Ali Ozmayi, kwamandan sojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC), ya jaddada a cikin wani sakon cewa: "Ni da dukkan mayakan sojin ruwa na dakarun IRGC kuma masu tsaron mashigar Hormuz, mun dauki alkawari ga Allah cewa, ta hanyar bin tafarkin shahidai, za mu ci gaba da tafarkin Shahidin Jagora cikin karfi da juriya. Muna da cikakken yakini cewa ramuwar gayyar Allah kan Amurka 'yar ta'adda da gwamnatin sahyoniya mara tushe ba ta da nisa, kuma tutar gaskiya za ta kasance a hannun magajinsa na kwarai kuma waliyyin zamani, za ta kuma kasance a kololuwar daukaka da iko."

Sakon Rear Admiral Ali Ozmayi, kwamandan sojin ruwa na dakarun kare juyin juya hali (IRGC) ga al'ummar musulmi, shi ne kamar haka:

«مِنَ الْمُؤْمِنِینَ رِجَالٌ صَدَقُوا مَا عَاهَدُوا اللَّهَ عَلَیْهِ فَمِنْهُمْ مَنْ قَضَی نَحْبَهُ وَ مِنْهُمْ مَنْ یَنْتَظِرُ وَ مَا بَدَّلُوا تَبْدِیلًا»

"A cikin muminai akwai mutanen da suka cika alkawarin da suka yi da Allah. Daga cikinsu akwai wanda ya kammala sadaukarwarsa (ya yi shahada), kuma daga cikinsu akwai wanda yake jiran (lokacinsa), kuma ba su canja ba."

Ya ku al'umma mai daraja da kuma al'ummar Iran mai sadaukarwa!

Aminci ya tabbata a gare ku.

Allahumma salli ala Muhammad wa ali Muhammad wa ajjil farajahum.

Shugaban al'ummar da ya yi shahada, wannan mutumi mai hakuri da basira, wannan muryar gaskiya mai karfi a gaban guguwar karya, wannan fitila mai haskaka shiriya a cikin duhun fitintinu, yanzu ya huta a kusa da rahamar Allah; amma sunansa, tunawarsa, tafarkinsa, da jininsa mai tsarki, za su kasance masu rai a cikin zuciyar wannan al'umma har abada.

A yau ba bankwana muke yi ba; a maimakon haka, muna sake sabunta alkawari ne da manufofinsa, da jajircewarsa, da imaninsa, da kuma tafarkin da ya ratsa daga kirjinsa har zuwa sararin samaniyar nan gaba mai haske.

Wannan bawan Allah na kwarai kuma mujahidi a tafarkin Allah, ya kare rayuwarsa ne a cikin tafarkin tabbatar da gaskiya, kare martabar al'ummar musulmi, da kuma tsare manufofin addinin Musulunci na Muhammadu (SAWA) mai tsarki, kuma tare da imani, basira da karfi, ya tsaya gaban rundunonin kafirci da girman kai, ya kuma sanya sunansa a cikin jerin mutanen da suka zama tarihi a wannan kasa.

Wannan babban mutumin na tarihi, ba kawai a fagen magana da tunani ba, har ma a fagen aiki, ya kasance mai kare martabar al'ummar musulmi da kuma mai kare mutuncin al'ummomi masu 'yanci. Muryarsa ta kasance amon gaskiya, kuma tafiyarsa tana nuna yakini da azama maras kakkautawa. Daga cikin mutanen da suka tsaya a sahun gaba na kare gaskiya a lokuta masu wuya na tarihi, ba don son zuciya ba, sai don dogaro ga yakini na Allah, ya kuma sanya sunansa a cikin littafin mujahidai a tafarkin Allah har abada.

A yau muna cikin jimami kan rashi mai zafi na wani babban mutum wanda mafi munin mutane a doron kasa suka shahadantar; wadancan makafi wadanda suke tsoron karfin ruhaniya, karfin magana da kuma ikon nazari na wannan shahidi mai daraja, kuma da yake ba su iya jure hasken imani da basirarsa ba, sai suka aikata wannan mummunan laifi. Wadannan makafi na girman kai da mabiya da suka rene su, ya kamata su sani cewa da wannan aika-aika ta rashin imani, ba kawai ba su sanya cikas a tafarkin gaskiya ba, har ma sun sanya kansu a cikin sahun mafi munin mutane a tarihi, a gaban adalcin Allah, kuma a gaban fushin wannan al'umma, sun kara kunyata kansu da kuma nuna kuskurensu.

Da zuciya mai bakin ciki da ruhi cike da jimami, muna mika ta'aziyyarmu ga fada mai tsarki na Hazrat Waliyyul Asr (AS), Jagoran juyin juya hali (D), al'ummar musulmi da dukkan masu 'yanci a duniya kan shahadar shugaba jarumi kuma Shahidin jagoran al'umma.

Ni da dukkan mayakan sojin ruwa na dakarun IRGC kuma masu tsaron mashigar Hormuz, muna daukar alkawari da Allah cewa, ta hanyar bin tafarkin shahidai, za mu ci gaba da tafarkin shugaban al'ummar da ya yi shahada tare da karfi da juriya. Muna da yakinin cewa ramuwar gayyar Allah kan Amurka 'yar ta'adda da gwamnatin sahyoniya mara tushe ba ta da nisa, kuma tutar gaskiya za ta kasance a hannun magajinsa na kwarai kuma waliyyin zamaninsa, za ta kuma kasance a kololuwar daukaka da iko.

Tunawa da sunan Imamimmu shahidi zai kasance a cikin littafin jarumai na al'ummar musulmi har abada. Ruhin wannan babban imam din ya kasance cikin rahamar Allah.

Rear Admiral Ali Ozmayi

Kwamandan sojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC)

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha