Talata 15 Satumba 2026 - 22:09
Koyar da Addini na Buƙatar Zurfin Fahimta da Sahihin Sanin Musulunci

Hauza/ Hujjatul Islam wal Muslimin Qazi Askar, mai kula da Harami Mai Tsarki na Hazrat Abdul'azim Hasani (A.S.), ya jaddada cewa koyar da addini ba aikin kowa ba ne. Ya ce mutanen da suke da alhakin wa’azi da koyar da ilimin addini dole ne su fara samun sahihiyar fahimtar Musulunci, sannan su bayyana shi ga mutane yadda ya kamata. Ya ƙara da cewa bai kamata a gabatar da addini ta hanyar da za ta sa mutane su nisanci Musulunci ba.

Hujjatul Islam Qazi Askar ya bayyana hakan ne a wata hira da wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Hauza a Tehran, inda ya yi nuni da shawarar Annabi Muhammad (S.A.W.A) ga Mu’az bn Jabal a lokacin da ya tura shi zuwa Yemen.

Ya ce lokacin da Annabi (S.A.W.A) ya tura Mu’az a matsayin wakilinsa, ya umarce shi da ya fara sanar da mutane Alƙur’ani, kyawawan ɗabi’un Musulunci, koyarwar addini da kuma tsarin rayuwa bisa imani. Haka kuma, ya jaddada masa muhimmancin tausasawa, adalci, kiyaye mutuncin ɗan Adam da kuma girmama haƙƙin mutane wajen mu’amala da su.

Sanar da mutane Littafin Allah

Hujjatul Islam Qazi Askar ya ce shawarar farko da Annabi (S.A.W.A) ya bayar ita ce a sanar da mutane Littafin Allah. Ya bayyana cewa wannan ba yana nufin karatun Alƙur’ani kawai ba ne, domin abin da ya fi muhimmanci bayan karatun shi ne yin tunani a kan ayoyinsa da kuma amfani da koyarwarsa a rayuwa.

Ya nuna takaici kan yadda a wasu lokuta ake takaita alaƙar mutane da Alƙur’ani kawai a wajen jana’iza ko bukukuwan aure, yayin da Alƙur’ani yake kasancewa a gidaje a matsayin abin ado ba tare da karantawa da yin tunani a kansa ba.

Ya ce idan muna son bin umarnin Annabi (S.A.W.A), dole ne mu karanta Alƙur’ani, mu yi tunani a kan ayoyinsa, sannan mu aiwatar da koyarwarsa a rayuwarmu.

Kyawawan ɗabi’un Musulunci da kiyaye haƙƙin kowa

Hujjatul Islam Qazi Askar ya ce ya kamata a koyar da mutane kyawawan ɗabi’un Musulunci. Ya bayyana cewa ƙarya, gulma, ɓata sunan mutane, take haƙƙin wasu da kuma ƙiyayya da juna ba su dace da ɗabi’un Musulunci ba.

Ya ce ya kamata a gina al’umma bisa mutunta juna da kyakkyawar mu’amala.

Ya bayyana cewa ra’ayin Musulunci game da mutane ya shafi kowa baki ɗaya. Gwamnatin Musulunci ba ta da alhakin kula da Musulmi da muminai kaɗai, a’a, tana da alhakin tabbatar da tsaro da kiyaye rayuwar duk mutanen da suke ƙarƙashin ikonta.

A nan ya yi nuni da wasiyyar Imam Ali (A.S.) ga Malikul Ashtar, inda ya ce mutane ko dai ’yan’uwa ne a addini ko kuma makamantansu ne a halitta. Ya ce saboda haka, ko wanda ba Musulmi ba dole ne a mutunta shi saboda shi ma ɗan Adam ne.

Ya bayyana cewa wannan cikakkiyar fahimtar Musulunci game da mutane za ta iya aiki a kowace irin al’umma.

Hujjatul Islam Qazi Askar ya kuma jaddada muhimmancin tausasawa wajen mu’amala da mutane. Ya ce Annabi (S.A.W.A) ya yi umarni da a yi wa mutane mu’amala cikin sauƙi da yafiya, sannan masu mulki kada su ɗora wa mutane abin da ya fi ƙarfinsu.

Ya ƙara da cewa hukunce-hukuncen laifuka da aiwatar da haddodi da sauran hukuntawa suna da nasu matsayi, amma ginshiƙin mu’amalar zamantakewa shi ne tausasawa da guje wa tashin hankali.

Sanin dukkan ɓangarorin Musulunci

Hujjatul Islam Qazi Askar ya jaddada cewa wajibi ne a gabatar da Musulunci cikin cikakkiyar siga, domin mutane su san dukkan muhimman koyarwarsa.

Ya ce ya kamata mutane su san akidojin Musulunci da koyarwarsa, tun daga Tauhidi, Ma’ad, Annabci da Imamai, har zuwa wajibai, haramun, mustahabbai da makaruhai.

Ya bayyana cewa ilimin addini na mutane da yawa ya kasance bisa al’ada kawai kuma yana da iyaka, don haka ana buƙatar zurfafa koyarwar addini tare da mayar da hankali kan yadda za a amfani da ita a rayuwa.

Ya kuma ce Sallah tana daga cikin manyan abubuwan da addini ya ba muhimmanci. Annabi (S.A.W.A) ya bayyana Sallah a matsayin shugabar Musulunci bayan mutum ya karɓi addini kuma ya yi ikirarin imani.

Hujjatul Islam Qazi Askar ya ce ya kamata a yi Sallah cikin nutsuwa da kulawa, tare da kasanto da zuciya a gaban Allah. A lokacin Sallah, mutum ya kamata ya ware kansa daga shagaltuwa da al’amuran duniya, ya mayar da hankalinsa ga Allah.

Tunatar da mutane Allah da Lahira

Hujjatul Islam Qazi Askar ya ce ya kamata a riƙa tunatar da mutane cewa Allah yana kallon ayyukansu, sannan rayuwar duniya ba ita ce ƙarshen rayuwa ba.

Ya ce ya kamata mutum ya tambayi kansa irin tanadin da ya yi wa Ranar Lahira, da kuma abin da zai gabatar a gaban Allah. Ya bayyana cewa wani lokaci tunatarwa ko nasiha guda ɗaya na iya sauya rayuwar mutum gaba ɗaya.

A matsayin misali, ya kawo labarin Fudail bn Iyad, wanda wata aya daga cikin Alƙur’ani ta yi tasiri sosai a kansa har ta sa ya tuba, sannan ya mayar wa masu dukiyar da ya taɓa ƙwace musu dukiyoyinsu.

Koyar da addini na buƙatar ƙwararru masu ilimi da sani

Hujjatul Islam Qazi Askar ya sake jaddada cewa koyar da addini ba aikin kowa ba ne. Ya ce mutanen da aka ɗora wa alhakin wa’azi da koyar da ilimin addini dole ne su fara fahimtar Musulunci yadda ya kamata, sannan su isar da shi ga mutane. Ya ce bai kamata a gabatar da addini ta hanyar da za ta sa mutane su nisanci Musulunci ba.

Ya yi nuni da wasu maganganun Imamai (A.S.) game da yadda ya kamata a gabatar da kyawawan koyarwar Ahlul Baiti (A.S.).

Ya ce Imam Rida (A.S.) ya bayyana cewa a koyi iliminsu sannan a sanar da mutane, domin idan mutane suka san kyawawan maganganun Ahlul Baiti (A.S.), za su bi su.

Saboda haka, Hujjatul Islam Qazi Askar ya ce wajibi ne a gabatar da Musulunci cikin hikima, tare da amfani da hujja, kyawawan ɗabi’u da kuma bayyana kyawawan abubuwan da addinin yake koyarwa.

Ya ƙare da cewa ƙungiyoyi irin su ISIS, waɗanda suka gabatar da mummunan hoto na Musulunci mai cike da tashin hankali, sun sa mutane da yawa suka nisanci Musulunci. A yayin da kuwa makarantar Ahlul Baiti (A.S.) take jaddada kyakkyawar mu’amala da mutane da kuma gabatar da kyawawan koyarwar addini.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha